Kundin tsarin mulki na 1999 ya yiwa kowane yankin Najeriya adalci - Buhari
Tanadin fuka-fukan adalci na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka shimfida a shekarar 1999, ya lullube dukkanin wani yanki da kasar nan ta kasa a cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce babu wani yanki a kasar nan wanda shimfidar kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ba ta yiwa lullubi na adalci ba.
Domin bayar da madogara ta tsayuwar sa a kan wannan lafazi, shugaban kasa Buhari ya hikaito tabbaci a kan hujjar kowace jiha cikin jihohi 36 da kasar nan ta kunsa ta samu wakili a bisa kujerar minista cikin majalisar zantarwa ta kasa.
Buhari yayin jaddada yaduwar adalci na kundin tsari mulki kasa, ya buga misali da yadda karamar jiha tamkar Bayelsa mai kananan hukumomi takwas kacal ke da Sanatoci uku a majalisar dattawa daidai na jihar Kano mai kunshe da kananan hukumomi 44.
Furucin shugaban kasa Buhari na zuwa ne a yayin da wata kungiya mai goyon bayan sa tare da mataikin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Buhari/Osinbajo Dynamic Support Group, ta ziyarci fadar sa ta Villa dake babban birni na tarayya a ranar Juma'a.
KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan jihar Oyo ya yi watsi da tayin kujerar minista a gwamnatin Buhari
Jagoran wannan tawaga, Usman Ibrahim, ya ce kungiyar su na daya daga cikin manyan kungiyoyi da suka taka muhimmiyar rawar gani wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari a yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.
A wani rahoton na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, mun samu cewa wani mahaifi a jihar Oyo, Wasiu Orilonise, ya shiga hannun hukuma bayan kama shi da laifin yiwa diyar sa fyade sau biyu a kowace rana. Ya amsa laifin sa da cewar yana aikata hakan ne domin tsare mata budurci.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng