Babbar Magana: Sabuwar Rigima Ta Barke Tsakanin APC Da Gwamnatin Kano Kan Abu 1

Babbar Magana: Sabuwar Rigima Ta Barke Tsakanin APC Da Gwamnatin Kano Kan Abu 1

  • Yayin da ake zaman jiran hukuncin kotun ƙoli kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano, sabuwar rigima ta kunno kai a jihar
  • Rigimar ta fara ne bayan jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin NNPP da ƙoƙatin karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar
  • Sai dai, gwamnatin NNPP ta yi martani inda ta ce zargin karkatar da kuɗaɗen wani yarfe ne kawai na siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnatin jihar Kano sun yi musayar yawo kan zargin wani shiri na karkatar da sama da naira biliyan 8 na kuɗin ƙananan hukumomin jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin karkatar da naira biliyan 8,080,190,875.13, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Kotun koli: Sabuwar zanga-zanga ta barke kan shari'ar gwamnan APC da dan takarar PDP

APC da gwamnatin Kano na sa'insa
APC da gwamnatin Kano na zargin juna kan karkatar da dukiyar gwamnati Hoto: Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A cewarsa rashin tabbas kan abin da zai kasance sakamakon hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan zaɓen gwamnan jihar ya sanya gwamnatin ɗaukar wannan matakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam’iyyar APC ya kuma gargadi ƙananan hukumomi da bankunan kasuwanci da su dakatar da shirin fitar da kuɗaɗen.

Wane martani gwamnatin Kano ta yi?

Jaridar Daily Trust ta ce da yake mayar da martani, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana cewa:

"Sannen abu ne cewa gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin ingantaccen shugabancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, a cikin watanni bakwai da suka gabata ta yi suna wajen ganin an tabbatar da gaskiya da adalci da amfani da dukiyar al'umma yadda ya dace."
"Domin haka ba abin mamaki ba ne kawai, har ma da cin fuska a yi tunanin cewa za ta yi sata ko kuma ta amince da irin wannan aika-aika, kamar yadda gwamnatin da ta shuɗe a jihar ta yi."

Kara karanta wannan

Ana dab da yanke hukunci, jam'iyyar APC ta bankado sabuwar kulla-kullar da gwamnatin Kano take yi

"Kuma gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba za ta bari mutanen da ke jin zafi ba wai domin faɗuwa zaɓe kaɗai ba, amma saboda sun yi asarar hanyoyin satar dukiyar gwamnati su ɗauke mata hankali ba."

Tsageru Sun Yi Yunƙurin Ƙona Gidan Gwamnatin Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bankaɗo shirin wasu tsageru na ƙona gidan gwamnatin jihar.

Rundunar ƴan sandan ta kuma bayyyana cewa tuni ta cafke tsagerun masu shirin aikata wannan ta'asar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng