‘Yan Majalisan Tarayya da Dokoki da Su Ka Mutu a Shekarar 2023 Kwanaki da Cin Zabe

‘Yan Majalisan Tarayya da Dokoki da Su Ka Mutu a Shekarar 2023 Kwanaki da Cin Zabe

  • Akwai ‘yan majalisan da su ka rasu tun a shekarar nan ta 2023, ‘yan watanni kadan bayan lashe zabe
  • Wasu daga cikin ‘yan siyasar nan sun mutu ne kafin su shiga ofis, wasunsu kuma ba su dade a kujerar ba
  • Daga baya hukumar INEC za ta shirya sabon zabe domin maye guraben wadannan ‘yan majalisar kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

1. Hon. Isma’ila Yushua Maihanchi

Kafin a kai ga rantsar da Hon. Isma’ila Yushua Maihanchi a majalisar wakilan tarayya, rai ya yi halinsa a farkon shekarar nan a Abuja.

Kafin nan, ana ta murnar Isma’ila Yushua Maihanchi ya lashe zabe ‘dan majalisa mai wakiltar mazabun Jalingo/Yorro/ Zing na jihar Taraba.

'Yan majalisa
Zaman wasu 'yan majalisa Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: Tsohon shugaban Majalisa, Ghali Na’Abba ya bar duniya

2. Hon. Abdulkadir Jelani Danbuga

Bayan shafe ‘yan watanni kadan a majalisar wakilai, sai ga labari maras dadi game da mutuwar Abdulkadir Jelani Danbuga daga Sokoto.

Honarabul Abdulkadir Danbuga ya rasu yana mai shekara 63 a yayin da yake wakiltar mutanen Isa da Sabon Birni a majalisar tarayya.

3. Nuhu Clark

Kafin a kai ga rantsar da Dr. Nuhu Clark sai ga rahoto cewa ‘dan siyasar ya rasu yayin da yake jinyar rashin lafiya a asibiti a kasar Indiya.

Clark ya lashe zabe a matsayin mai wakiltar mazabar Chibok a jihar Borno a majalisar dokoki, saura watanni uku ya shiga ofis ya rasu.

4. Madami Garba Madami

Ko da aka rantsar da ‘yan majalisar dokoki a jihar Kaduna, Madami Garba Madami bai samu halarta ba saboda yana fama da rashin lafiya.

Rahotanni sun ce sabon ‘dan majalisar na yankin Chikun yana cikin ‘yan majalisa ta goma da aka rasa tun a shekarar farko a ofis a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kaddara ta riga fata: Jerin 'yan takara 9 da suka mutu daf da shirye-shiryen zabe a 2023

Majalisa: Menene abin da doka ta ce?

Da zarar majalisa ta sanar da INEC, hukumar za ta shirya sabon zabe domin maye guraben wadannan ‘yan majalisar tarayya da na dokoki.

Sashe na 34 na dokar zaben 2022 ya ce idan ‘dan takara ya mutu kafin fara zabe, INEC za ta dakata na kwana 14 jam’iyya ta canza ‘dan takara.

Idan bayan an shiga zabe ne sai ‘dan takara ya mutu, za a dauko abokin gaminsa.

'Yan siyasan da su ka mutu a 2023

Kuna da labari cewa manyan ‘yan takaran LP, PDP da NNPP da su ka rasu a shekarar nan ta 2023 sun hada da Farfesa Uche Ikonne a jihar Abia.

Ana shirye-shiryen zaben shekara nan ‘yan bindiga su ka kona ‘dan takaran Sanatan LP a Enugu, a dalilin haka dole INEC ta dakatar da zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng