Ana Dab da Yanke Hukunci, Jam'iyyar APC Ta Bankado Sabuwar Kulla-Kullar da Gwamnatin Kano Take Yi
- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Kano ta yi magana kan shirin gwamnatin jihar na wawushe N8bn daga asusun jihar
- Jam'iyyar ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta umarci ƙananan hukumomin jihar da su fitar da kuɗaɗen domin aikin wasu gadojin sama
- APC ta ce sam aikin va dace ba domin a cewarta wani shiri ne kawai na yin almubazzaranci da dukiyar mutanen jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ƙano ta bankaɗo wani shiri da wasu jami’an gwamnatin jihar Kano suka yi na wawushe naira biliyan 8,080,190,875.13 daga asusun gwamnatin jihar Kano.
Shugaban jam'iyyar na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar da kada su shiga cikin yunƙurin da wasu jami’an gwamnatin ke yi, cewar rahoton The Guardian.
Ya kuma gargaɗi bankunan kasuwanci da ke da hannu a cikin yarjejeniyar da su dakatar da aikin fitar da kuɗaɗen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsayin jam’iyyar APC na zuwa ne bayan hukuncin da kotun ƙoli ta tanada a shari'ar gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
Wane zargi jam'iyyar APC ta yi?
Jaridar Leadership ta ce shugaban na APC a wata sanarwa da ya fitar ya ce yana da kwafin takardar amincewa da ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi ta umurci ƙananan hukumomi 44 da su fitar da da kuɗaden.
A cewarsa an umarci ƙananan hukumomin da su fitar da Naira miliyan 101,655,000.38 da kuma Naira miliyan 3,607,370,858.00 kowannensu domin gina gadojin sama na Dan Agundi da Tal'udu.
Shugaban Jam’iyyar ya bayyana cewa a ranar Juma’a ne gwamnati ta cire tare da sanya sabbin daraktoci da ma’ajiyoyi domin tabbatar da cewa ba a samu cikas wajen murɗe ƙananan hukumomin ta hanyar almubazzaranci da kuɗaɗensu ba.
Ya bayyana cewa yanke shawarar fara gudanar da irin waɗannan ayyuka a wannan lokaci hatta mutanen da ke cikin jam’iyyar NNPP sun yi Allah wadai da ita.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sake duba lamarin domin ci gaban jihar Kano.
An Faɗi Kuskuren Abba Wajen Rusau a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani lauya wasu lauyoyi sun bayyana kuskuren Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen yin rusau a Kano.
Lauyoyin sun yi nuni da cewa a hurumin doka akwai ƙa'idojin da ake bi kafin a ruguza gine-ginen mutane.
Asali: Legit.ng