PDP Ta Fusata Kan Shirin Gwamnanta na Yi Wa Tinubu Biyayya, Ta Aike da Gargadi Mai Zafi

PDP Ta Fusata Kan Shirin Gwamnanta na Yi Wa Tinubu Biyayya, Ta Aike da Gargadi Mai Zafi

  • Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na ƙasa ya gargaɗi Gwamna Sim Fubara kan aiwatar da yarjejeniyar da ya sanya wa hannu ba tare da sanin jam'iyyar ba
  • Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na ƙasa, Timothy Osadolor, ya ce batutuwan da ake rigima a kansu sun wuce sanin Gwamna Fubara
  • Osadolor ya ce jam’iyyar PDP tana gaban kotu domin ƙalubalantar lamarin saboda akwai batutuwan da suka shafi tsarin mulki ba a hannun gwamnan ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na ƙasa, Timothy Osadolor, ya ce gwamna Sim Fubara ba zai iya aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da ya amince da shi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Kano: Daga karshe Ganduje ya yi magana kan hukuncin kotu a shari'ar zaben Doguwa

Osadolar ya ce batutuwan da ake tattaunawa sun fi ƙarfin Fubara saboda batutuwa ne da suka shafi kundin tsarin mulki.

PDP ta gargadi Gwamna Fubara
Shugaba Tinubu ya jagoranci cimma yarjejeniya tsakanin Wike da Fubara Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar The Punch a ranar Talata, 26 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane gargaɗi Osadalor ya yi wa Fubara?

Jigon na PDP ya ce Gwamna Fubara ya kamata ya san iyakarsa kuma ya tsaya a kan iyakar ikonsa.

Osadolor ya bayyana cewa jam’iyyar PDP tana gaban kotu domin kare kujerunta na ƴan majalisar da suka sauya sheƙa, saboda ƙuri’un da suka samu na jam'iyyar ne ba na ƴan majalisar ba ko na Fubara da shugaban ƙasa ba.

A kalamansa:

“Amma batutuwan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke damun kansa sun fi shi girma. Sun kuma fi gwamna girma saboda batutuwan da suka shafi kundin tsarin mulki ne."

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

"Kujerun ƴan majalisar da suka sauya sheƙa babu kowa a kansu, batu ne da ya shafi kundin tsarin mulki, ba bisa ga ra'ayin Shugaba Tinubu ko wani mutum ba. Al'amari ne na kundin tsarin mulki ƙarara."

'PDP ke da hurumi kan kujerun ƴan majalisar' - Osadalor

Osadalor ya cigaba da cewa:

Hakazalika, a kundin tsarin mulki PDP ce ke da ƙuri'un, saboda haka ban ga ta yadda Gwamna Fubara zai gaya wa PDP saboda ya gana da shugaban ƙasa a Aso Rock cewa kada ta kula da ƙuri'unta. A yanzu haka PDP na kotu, ƙuri'un na PDP ne, ba na Fubara ko Villa ba."
"Abin da gwamnan ke da hurumin yi shi ne ya biya albashi da alawus ɗin ƴan majalisar har zuwa ranar da kujerunsu suka zama babu kowa. Na tabbata cewa gwamnan ya san iyakar matsayinsa."

Sule Lamido Ya Magantu Kan Rikicin Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan yarjejeniya takwas da aka ƙulla tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.

Lamido ya yi fatali da yarjejeniyar tare da caccakar kwamitin gudanarwa na ƙasa na PDP kan yadda ya bari Shugaba Tinubu ya tsoma baki kan rikicin da ya shafi jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng