Kwanaki Bayan Samun Babbar Sarautar Gargajiya, El-Rufai Ya Ziyarci Obasanjo

Kwanaki Bayan Samun Babbar Sarautar Gargajiya, El-Rufai Ya Ziyarci Obasanjo

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya bayyana kai ziyara ga babban mai gidansa, shugaba Olusegun Obasanjo
  • Ya yada hotunan da ke nuna yadda ya samu tarba a gidan nasa kwanaki kadan bayan an nada shi sarauta
  • El-Rufai ya rike mukamai har guda biyu a mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abeokuta, jihar Ogun - Mallam Nasiru El-Rufai ya kai ziyara ga tsohon uban gidansa, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta ta jihar Ogun.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka nada El-Rufai wata sarautar gargajiya a kasar nan.

El-Rufai ya gana da Obasanjo
Yadda El-Rufai ya ziyarci Obasanjo | Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Wacce irin ziyara ya kai?

Da yake bayyana ziyarar a shafinsa na Twitter, tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana irin tarbar da ya samu a gidan mai gidan nasa.

Kara karanta wannan

"Na iya bakin kokarina a matsayin shugaban kasar Najeriya", Ibrahim Babangida

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"A yau dinna, na ziyarci mai gida na. Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tarbe ni da abokaina zuwa gidansa da ke Abeokuta. Mun samu tarba ta musamman daga matar Obasanjo da ta shirya mana abincin rana muna godiya. Sai kuma Kirsimeti da yardar Allah."

Meye alakar El-Rufai da Obasanjo?

A zamanin Obasanjo, El-Rufai ya yi aiki a matsayin babban daraktan BPE wanda daga baya aka ba shi mukamin minista.

A 2019, Obasanjo ya siffanta Malam Nasiru a matsayin daya daga mutanen da suka kware kuma kwanaye da ya yi aiki dasu.

Idan baku manta ba, El-Rufai ya yi gwamna a jihar Kaduna har sau biyu, inda daga baya Tinubu ya nemi a tantance shi a matsayin minista, hakan bai ga nasara ba.

Hakan ya jawo cece-kuce da dasa ayoyin tambaya game da makomar siyasarsa a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Waiwayen shekara: Jerin yan siyasar Najeriya mafi shahara a 2023

El-Rufai da rashin minista

Tun kafin Shugaban kasa ya janye sunansa ko ya sake maidawa a cikin ministoci, sai aka ji Nasir El-Rufai ya tattara ya bar Najeriya.

Daily Trust ta ce an yi tunanin Nasir El-Rufai zai zama Ministan lantarki da makamashi a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, sai lamari ya canza.

Tun a ranar Juma’a, jagoran na jam’iyyar APC ma-ci ya bar Najeriya zuwa Masar, ya kuma nunawa shugaban kasa bai sha’awar ya rike mukami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.