Tsohon Gwamna Ya Bayyana Babban Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Binciki Buhari
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa yana son shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya binciki tsohon Shugaba Buhari
- A cewar Bafarawa matsalolin da ƙasar nan ke ciki Tinubu ya gaje su ne a wajen gwamnatin Buhari wacce ta shuɗe
- Bafarawa ya yi nuni da cewa idan Tinubu bai binciki Buhari ba duk laifin da aka yi a gwamnatin baya kan shi zai dawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya yi magana kan halin da ƙasar nan ke ciki a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu.
Tsohon gwamnan a yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Punch ya yi magana kan abubuwan da suka shafi ƙasa.
A yayin tattaunawar, Bafarawa ya yi magana kan halin Tinubu ya amshi ƙasar nan a hannun tsohon Shugaba Buhari, da buƙatar binciken gwamnatin tsohon shugaban ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bafarawa ya bayyana cewa matsalolin da ake fama da su a ƙasar nan gadarsu aka yi daga gwamnatin da ta wuce.
'Laifin Buhari ne matsalolin da ƙasar nan ke ciki' - Bafarawa
A cewar tsohon gwamnan Buhari ya kamata a ɗorawa alhakin duk wahalwahalun da ƴan Najeriya suke sha ba Shugaba Tinubu ba.
A kalamansa:
"Ban ga dalilin da zai sa gwamnatin Tinubu ba za ta binciki Buhari ba. Hasali ma Buhari ne mutum na farko da ya kamata a fara bincike domin lokacin da ƴan Najeriya suka zaɓe shi sun zaɓi gaskiya."
"Buhari ya shaidawa ƴan Najeriya cewa shi ne mafi gaskiya mai amana. A lokacin da shi (Buhari) yake yaƙin neman zaɓe, ya ce shi ne mai gaskiya, mafi tsafta da sauransu. Yanzu, ya yi shekaru takwas, kuma ya tafi."
"Domin haka, zai zama babban kuskure kuma ba zai taimaki ƙasar nan ba idan Tinubu ya gaza bincikar gwamnatin Buhari. Idan yana son ya tsira daga zargi, sai ya binciki gwamnatin da ta shuɗe."
"Idan aka samu Buhari baya da laifi to mutane za su yi farin ciki da shi. Amma idan aka same shi yana da laifi, sai ya amsa laifinsa. Amma ba zai yi kyau ƴan Najeriya su bar Buhari ya tafi haka ba."
"Idan har Shugaba Tinubu ya kyale Buhari ya tafi ba tare da bincikarsa ba, to ya kamata (Tinubu) ya sani cewa duk abin da Buhari ya yi a lokacin yana gwamnati, za a ga Tinubu a matsayin wanda shi ne ya yi su."
Bincike Ya Iso Kan Ministar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa binciken da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) take yi ya isa kan Sadiya Umar Farouk, tsohuwar ministar jin ƙai a gwamnatin Buhari.
Hukumar ta EFCC ta gano N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar a ƙarƙashin Sadiya Umar-Farouk.
Asali: Legit.ng