Rikicin PDP: Tinubu Ya Tilasta Gwamna Fubara Sa Hannu Kan Yarjejeniya? Shugaban PDP Ya Fadi Gaskiya

Rikicin PDP: Tinubu Ya Tilasta Gwamna Fubara Sa Hannu Kan Yarjejeniya? Shugaban PDP Ya Fadi Gaskiya

  • Muƙaddashin shugaban PDP na jihar Rivers, Chukwuma Aaron, ya yi watsi da batun cewa Gwamna Fubara ya sanya hannu kan yarjejeniya takwas na Shugaba Tinubu bisa tursasawa
  • Aaron, yayin da yake jawabi ga masu zanga-zangar adawa da Nyesom Wike, ya ce an amince da yarjejeniyr tare da sanya hannun manyan masu ruwa da tsaki a jihar ciki har da Gwamna Fubara da shi
  • David Briggs, tsohon kwamishina a jihar, ya yi iƙirarin cewa yana cikin taron, kuma kawai Tinubu ya kawo rubutacciyar takarda domin Fubara ya sanya hannu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Shugaban riƙo na jam’iyyar PDP a jihar Rivers, Chukwuma Aaron, ya yi jawabi ga masu zanga-zangar da ke rera waƙar yabon Gwamna Siminalayi Fubara tare da yin Allah wadai da Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan arewa ya haddasa sabon rikici a jam'iyyar PDP, an fara musayar yawu

A cikin jawabinsa, ya ce Gwamna Fubara bai sanya hannu bisa tilastawa kan yarjejeniyar da Shugaba Tinubu ya jagoranta, kamar yadda tsohon kwamishinan ayyuka a jihar, David Briggs ya yi iƙirari, wanda tun da farko iƙirarinsa ya jawo zanga-zangar.

Shugaban PDP ya yi magana kan yarjejeniyar Wike da Fubara
Shugaba Tinuɓbu ya jagoranci cimma yarjejeniya tsakanin Fubara da Wike Hoto: Nyesom Wike, Bola Ahmed Tinubu, Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Aaron ya ce ya wahalta ma PDP ba kamar yadda Briggs da wasu ke rura wutar siyasa tsakanin gwamnan da ubangidansa Wike ba, domin ya kasance a PDP tsawon rayuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rivers jiha ce ta PDP, shugaban riko ya haƙiƙance

A cewar Aarom, jam’iyyar PDP gida ɗaya ce, jihar Rivers kuma ta PDP ce. Ya yi watsi da iƙirarin cewa nan ba da jimawa ba shi da Wike za su fice daga PDP zuwa APC, inda ya ƙara da cewa babu gaskiya a cikin wannan zargi.

A cikin wani furuci mai zafi, Aaron ya cigaba da cewa Briggs bai taɓa zama cikakken ɗan PDP ba, domin haka bai kamata a amince da irin wannan mutumin ba kuma a saurare shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Zanga-zanga ta ɓarke a gidan gwamnatin jihar PDP kan muhimmin batu

Ya jaddada cewa yana ɗaya daga cikin waɗanda suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar a fadar shugaban ƙasa a lokacin da shugaba Tinubu ya yi wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jihar Rivers.

Muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP ya ce ya sanya hannu ne saboda gwamnan ya yi hakan, kuma babu wanda ya fuskanci matsin lamba a lokacin tattaunawar.

Dattawan Rivers Sun Maka Tinubu Kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dattawan jihar Rivers sun kai ƙarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ƙara a gaban kotu.

Dattawan waɗanda suka maka Tinubu ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, sun yi hakan ne bisa tilasta Gwamna Fubara shiga yarjejeniya da Wike da Shugaba Tinubu ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng