Jerin Manyan Ƴan Siyasar Najeriya da Kotu Ta Yanke Wa Hukuncin Zaman Gidan Gyaran Hali a 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kowane mutum yana son a masa adalci amma a wasu lokutan zaku ga ɗan siyasa a Najeriya ya tsinci kansa a gidan gyaran hali bisa wani laifi da ya aikata.
Duba da yadda cin hanci ya yi wa ƙasar nan katutu, karkatar kuɗin baitul mali da kesa-kesan bogi ba sabbin laifuka bane, sayen kuri'u da sauransu, ya kamata a ce kotu ta ɗaure ƴan siyasa fiye da yadda aka gani a 2023.
Sai dai duk da waɗannan laifuka, ƴan siyasa suna da hanyar da suke kubuta daga irin waɗan shari'o'in ta hanyar amfani da lauyoyi manya da zasu kare su a kotu.
Legit Hausa ta tattaro muku manyan ƴan siyasa biyu da kotu ta sa suka girbi laifukan da suka shuka a shekarar 2023, ga su kamar haka:
Nazarin shekara: Shugaba Tinubu da wasu manya jigan-jigan siyasa da suka samu gagarumar nasara a 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ike Ekweremadu
Mutum na farko da zai fara zuwa zuciyar ƴan Najeriya shi ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, wanda aka yi wa ɗaurin shekara tara da watanni takwas a Burtaniya.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, kotu ta yanke wannan hukukci a ranar 5 ga watan Mayu, 2023 bayan ta kama Ekweremadu da laifin safarar sassan jikin ɗan adam.
Kotun ta kama Ekweremadu, matarsa da likitansu, Obinna Obeta da laifin haɗa baki wajen ɗauko matashi ɗan shekara 21 daga Legas zuwa Landan domin cire masa ƙoda.
Sun kai matashin mai saye da siyarwa a kan titin Legas ƙasar Burtaniya ne da nufin cire masa koda ɗaya a sanya wa ɗiyar babban ɗan siyasan mai suna, Sonia.
Wahab Hammed
A ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba, 2023 aka ɗaure shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Surulere ta jihar Legas, tsawon shekara ɗaya a gidan gyaran hali.
Mai shari'a Isma'il Ijelu na babbar kotun jihar Legas mai zama a Ikeja, shi ne ya yanke wannan hukunci bayan kama Wahab da laifuka biyu na haɗa baki da cin hanci.
A cewar mai shigar da ƙara na hukumar yaƙi da rashawa EFCC, Samuel Daji, jigon APC ya haɗa kai da wani Segun Ijitola, suka riƙa siyan kuri'u a zaben shugaban ƙasa da na yan majalisar tarayya.
Amma mai shari'a Ijelu ya baiwa jigon APC mai mulki zaɓin biyan tara na Naira Miliyan ɗaya.
Tsohon gwamna ta tada hazo a PDP
A wani rahoton na daban kuma Kalaman tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, kan rikicin jihar Ribas sun haddasa kace-nace a jam'iyyar PDP
Yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta zargi Lamido da yi wa APC aiki, PDP ta Jigawa ta fito ta karyata ikirarin.
Asali: Legit.ng