Tsohon Gwamnan Arewa Ya Haddasa Sabon Rikici a Jam'iyyar PDP, An Fara Musayar Yawu
- Kalaman tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, kan rikicin jihar Ribas sun haddasa kace-nace a jam'iyyar PDP
- Yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta zargi Lamido da yi wa APC aiki, PDP ta Jigawa ta fito ta karyata ikirarin
- Shugaban PDP na jihar Jigawa ya ce ikirarin uwar jam'iyya barkwanci ne kawai da yake neman wuce gona da iri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya haddada musayar yawu tsakanin shugabannin jam'iyyar PDP kan kalaman da ya yi game da rikicin jihar Ribas.
Ranar Laraba da ta gabata, Lamido ya shawarci Gwamna Siminalayi Fubara ya yi watsi da yarjejeniya 8 da aka cimma wa yayin sulhun shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Ya kuma caccaki kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa bisa yadda suka gaza shawo kan rikicin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Fubara, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ga dukkan alamu kalamansa ba su yi wa NWC daɗi ba, inda aka ji sakataren watsa labaran PDP ta ƙasa ya fito yana zargin Lamido da yi wa APC aiƙi.
PDP reshen Jigawa ta maida martani
Da take martani PDP ta jihar Jigawa ta musanta ikirari da kwamitin gudanarwa NWC cewa tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido yana yi wa jam’iyyar APC aiki.
Alhaji Isa Bello, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Dutse ranar Juma’a, 22 ga watan Disamba, 2023.
A kalamansa ya ce:
"Maganar cewa Lamido yana yiwa APC aiki, wasam barkwanci ne da ya wuce gona da iri kuma mu a Jigawa an gina mu ne kan tafarkin fafutukar kare hakkin talaka da adalci."
Bello ya bukaci mambobin kwamitin NWC na ƙasa da su dauki shawarar Lamido da muhimmanci wajen karfafa jam’iyyar PDP, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Tsohon shugaban APC ya magantu kan cire tallafin mai
A wani rahoton kuma Bisi Akande, tsohon shugaban APC na rikon kwarya ya ce Muhammadu Buhari ya kamata a ce ya cire tallafi tun farko.
Akande, tsohon gwamanan jihar Osun ya ce da an cire tallafin a lokacin Buhari da yan Najeriya ba zasu wahala a lokacin Tinubu ba.
Asali: Legit.ng