Rusa Zaben Abba Kabir: Jerin Hukunce-Hukuncen Kotu da Suka Bai Wa Mutane Mamaki a 2023

Rusa Zaben Abba Kabir: Jerin Hukunce-Hukuncen Kotu da Suka Bai Wa Mutane Mamaki a 2023

Ya kamata kotu ta zama kafar da za ta kwata wa dan Najeriya hakkinsa, amma wasu hukunce-hukuncen kotun zabe sun bai wa 'yan kasar mamaki.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yayin da shekarar 2023 ta zo karshe, akwai wasu hukunce-hukuncen kotuna da suka bai wa mutane mamaki bayan zartar da hukunci.

Jerin Hukunce-hukuncen Kotu da Suka Ba da Mamaki a 2023
Shekarar 2023 ta zo da wasu abubuwan mamaki a shari'ar zabe. Hoto: Caleb Mutfwang, Abba Kabir, Ahmad Lawan.
Asali: Twitter

Jerin hukunce-hukuncen kotun

Legit Hausa ta jero muku irin wadannan hukunce-hukunce sa suka faru a kasar a wannan shekara da muke ciki:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ahmad Lawan vs Machina

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan bai yi takarar tsayawa sanatan Yobe ta Arewa ba amma an sanar da shi a Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun ta tsare matashi kan zargin caka wa abokinsa wuka a ciki, wanda ake zargi ya magantu

Bashir Machina wanda shi ne sahihin dan takarar dole ya shiga sharia don kare kujerarshi a babbar Kotun Tarayya.

Daga bisani APC da Lawan sun garzaya Kotun Koli inda suka yi nasara.

Masana shari'a da sauran mutane sun yi Allah wadai da irin wannan hukunci da aka yanke.

2. Abba Kabir vs Gawuna

Wani abin da yafi bai wa mutane mamaki shi ne kwace kujerar Gwamna Abba Kabir a jihar Kano.

Kotun zabe ta rusa zaben gwamnan da kwashe kuri'u dubu 165 saboda rashin ingancinsu.

Har ila yau, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin da cewa Abba ba dan jam'iyyar NNPP ba ne.

A jiya Alhamis, Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben jihar inda yanzu ake dakon hukuncin karshe.

3. Mutfwang vs Goshwe

Wani abin mamaki kuma shi ne shari'ar zaben jihar Plateau tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang da Nentawe Goshwe.

Kara karanta wannan

An daure matashi shekaru 75 a gidan kaso kan zargin damfarar biliyan 1, ya yi ta maza

Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben Gwamna Caleb da hujjar cewa jami'yyar PDP ba ta da tsari a jihar.

Dan takarar jam'iyyar APC a jihar, Nentawe Goshwe shi ke kalubalantar zaben Gwamna Caleb da cewa an tafka magudi.

A farkon shekarar 2024 ce ake saran Kotun Koli za ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar zaben gwamnan jihar.

4. 'Yan Majalisun Tarayya da jihohi a Plateau

Kamar yadda kotu ta yi hukunci a shari'ar zaben gwamnan Plateau, ta rusa dukkan zaben 'yan Majalisun PDP a jihar.

Dukkan kujerun 'yan Majalisun Tarayya da na jihohi an kwace su da hujjar cewa jami'yyar ba ta da tsari a jihar kan daukar nauyin 'yan takara.

Jerin abubuwa marasa dadi 8 da suka faru a 2023

A wani labarin, ko wace shekara tana zuwa da kalubale a cikinta wanda ke tayar wa da mutane hankali

A wannan rahoto, Legit Hausa ta jero muku wasu iftila'in da suka faru a wannan shekara da tazo karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.