Abin da Ya Faru Tsakanin Lauyoyin Abba, NNPP, INEC Da Lauyan APC a Kotun Koli a Yau

Abin da Ya Faru Tsakanin Lauyoyin Abba, NNPP, INEC Da Lauyan APC a Kotun Koli a Yau

  • Wole Olanipekun ya ce kuri’un da aka sokewa NNPP sun fito da su daga kotu ne kuma babu wanda ya yi maganarsu
  • Lauyan NNPP, Adegboyega Awomolo, ya fadawa Kotun Koli babu dalilin a azabtar da mutane saboda kuskuren INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Kotun Koli ta saurari shari’ar zaben gwamnan jihar Kano a karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro yau Alhamis.

Wole Olanipekun (SAN) ya fadawa kotun koli a yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara da ya ce Abba Kabir Yusuf ba ‘dan NNPP ba ne.

Shari'ar Kano a kotun koli
Abba, NNPP da Nasiru Gawuna sun je Kotun koli Hoto: Abba Kabir Yusuf, IU_Wakilii, supremecourt.gov.ng
Asali: UGC

Ra'ayin lauyan Abba Kabir Yusuf

Punch ta ce Wole Olanipekun (SAN) ya yi ikirarin ba za ayi aiki da ka’idojin hukumar INEC a soke zabe saboda rashin sa hannu a kuri’u ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

An saurari karar Abba, Kotun Koli za ta yanke hukunci a shari’ar gwamnan Kano

Lauyan na gwamnan Kano ya bukaci babban kotun ta raba gardama kan hurumin alkalai na rusa zaben da aka yi nasara da rata mai yawa

Mai shari’a John Okoro ya tambayi abin da ya faru a shari’o’in baya, masu kare Abba Kabir Yusuf sun ce sam ba ayi wa gwamnan adalci ba.

Kotun koli ta tambayi kuri'un NNPP da aka soke

Alkalin ya tambayi Lauyan ko an kawo maganar kuri’un da aka soke a kananan kotunan, Olanipekun ya ce sam alkalai ba su yi hakan ba.

“Babu wanda ya gabato da maganar sahihancin kuri’un nan. Sun fito da su daga kotu ne. Babu wanda ya yi magana a kai.”

- Wole Olanipekun

John Okoro ya tambaya ko kuri’un da aka sokewa NNPP halatattu ne, sai Olanipekun ya sake tabbatarwa kotu daga hannun INEC su ka fito.

Akin Olujimi mai kare APC ya fadawa kotun an saba ka’idar INEC domin kotun korafin zabe ta gano ba a sa hannu a bayan kuri’un ba.

Kara karanta wannan

‘Yan Kwankwasiyya, Masoyan Abba sun tashi da azumi domin yin nasara a Kotun koli

Gwamna Abba 'dan NNPP ne?

A game da maganar jam’iyya, Olujimi SAN ya ce babu sunan Abba Yusuf a rajistar NNPP.

Rahoton ya ce lauyan INEC, A.B Mahmoud, SAN ya fadawa kotu cewa kuri’un da ake magana daga hannun hukumarsa su ka fito da zabe.

A.B Mahmoud SAN ya ce ba aikin mai zabe ba ne ya duba ko akwai kwanan wata da sa hannu a takardar zabe yayin da zai kada kuri’arsa.

A.B Mahmoud SAN ya kara da cewa ba a kotu aka duba kuri’un ba, a ofishin alkalai ne.

Kano: NNPP sun yi korafi a kotun koli

Shi ma lauyan NNPP, Adegboyega Awomolo yana ganin kotu sun wuce gona da iri wajen soke zaben da ba Nasiru Yusuf Gawuna nasara.

Awomolo ya fadawa alkalai cewa ba a fadi rumfunan zaben da aka fito da kuri’un ba, kuma bai kamata a azabtar da masu zabe a Kano ba.

Lauyan na NNPP bai ganin za a iya soke kuri’un mutane 165,165 da su ka zabi jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Kotun koli ta tsaida ranar sauraron shari’ar zaben Gwamnan Kano

Yaushe za ayi hukunci a kan zaben Kano?

Nan da kwanaki za a san wanda ya yi nasara a shari'ar da ake yi a kan zaben Gwamnan Kano bayan gama sauraron karar a kotun koli.

Inyang Okoro wanda ya yi hukunci a shari’ar Bola Ahmed Tinubu da PDP zaben 2023 ya jagoranci zaman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng