Manyan Hasashen Siyasa da Aka Yi Wadanda Ba Su Faru Ba a 2023
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - A cikin 2023, fastoci da yawa na Najeriya sun fitar da hasashe da ke bayyana abin da suka yi iƙirarin cewa "Allah ya faɗa musu" zai faru.
Yayin da wasu hasashen sun faru, wasu ba su faru ba.
A yayin da ƙarshen shekarar 2023 ke ƙara ƙaratowa, Legit.ng ta duba wasu daga cikin manyan hasashen na siyasa da suka gaza - wato - waɗanda ba su faru ba.
1) 'Ba za a rantsar da Tinubu ba': Bishop Daniels
Wanda ya kafa cocin ‘I Reign Christian Ministry’, Feyi Daniels, ya yi hasashen cewa Bola Tinubu ne zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai malamin ya bayyana cewa ba za a rantsar da Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023 ba, maimakon haka jami’an tsaro za su kama shi, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Binciken da Legit.ng ta yi a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, ya nuna cewa Daniels gaba ɗaya ya samu kuskure a hasashensa.
2) 'Gwamnatin wucin gadi daga Mayun 2023' - Fasto Chidi
A watan Yulin 2022, Fasto Godfrey Chidi, ya ce za a samu gwamnatin wucin gadi daga ranar 29, ga watan Mayun 2023.
Ya bayyana cewa ya hango mummunar makoma a 2023. Ya zuwa watan Disamban 2023, Najeriya ba ta ƙarƙashin gwamnatin wucin gadi, saɓanin hasashensa.
3) Pastor Kingsley Okwuwe
A watan Agusta, Fasto Kingsley Okwuwe na cocin Revival and Restoration Global Mission ya yi hasashen cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), zai yi nasara a kotu.
Malamin ya yi hasashen cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa (PEPT) za ta soke nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Amma bayan duka kammala fafatawa a kotun zaɓen da kotun ƙoli, Obi bai yi nasara a kotu ko ɗaya ba.
4) Fasto Naomi George
Gabanin hukuncin da kotun ƙoli ta yanke game da zaɓen shugaban ƙasa na 2023 mai cike da takaddama a Najeriya, Evangelist Naomi George ta ce nan ba da jimawa ba za a ayyana Obi a matsayin shugaban ƙasa.
A cikin kalamanta:
"Tinubu zai sauka domin Obi ya karɓi mulki."
A halin yanzu, bisa dokokin Najeriya, ba zai taɓa yiwuwa Shugaba Tinubu ya yi murabus ba domin Obi ya hau mulki.
Idan har akwai wani dalili da zai sa Tinubu ya “ya yi murabus”, Obi ba ya cikin waɗanda za su gaje shi domin shi (Obi) ba zaɓaɓɓe bane kuma ba ɗan jami'iyya mai mulki ba ne.
5) Fasto Christiana Eunice
Kwana ɗaya gabanin hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba 6 ga watan Satumba, Prophetess Christiana Eunice, wacce ta kafa Covenant Of God Church Praise Sacrament, ta ce Obi zaɓin Allah ne.
Da take magana a gidan Talabijin na WomanOfGod, Fasto Eunice ta ce gwamnatin APC "ba abin da ƴan Najeriya suke tunani ba ne", inda ta bayyana jam'iyyar a matsayin "baƙa" wacce take nuna kanta a matsayin "fara"
6) Fasto Ishaya Wealth
Bayan ƙararrakin da suka biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Fasto Isaiah Wealth ya yi hasashen samun nasara ga Obi.
Wealth a yayin hidimar coci, ya ce idan Obi ya gabatar da "shaidar da ta dace" a kotu, za a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Faston wanda shi ne jagoran wa’azi a Isaiah Wealth Ministries ya kuma bayyana cewa shugaba Tinubu ne ya zo na uku a zaɓen yayin da Atiku Abubakar da Obi suka zo na biyu da na ɗaya.
Manyan Ƴan Siyasan da Suka Shahara a 2023
A wani labarin kuma, mun tattaro muku manyan ƴan siyasan da suka shahara a shekarar 2023, wacce a cikinta aka gudanar da babban zaɓe a Najeriya.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na daga cikin ƴan siyasan da suka yi suna a 2023.
Asali: Legit.ng