Kotun Koli: Ana Dab da Fara Shari'a, Gawuna Ya Samu Gagarumin Goyon Baya
- A yayin da ake dab da fara zaman sauraron shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kano a kotun ƙoli, wasu ɗalibai sun nuna goyon bayansu ga Gawuna
- Ƙungiyar ɗaliban ta nesanta kanta da zanga-zangar da wasu magoya bayan jam'iyyar NNPP suke yi a jihar
- Ɗaliban sun kuma buƙaci al'ummar jihar Kano da su nuna goyon bayansu ga Gawuna a shari'ar da yake da Gwamna Abba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ƙungiyar wasu ɗaliban Kano ta buƙaci al’ummar jihar da su yi watsi da yunƙurin da ake zargin magoya bayan jam’iyyar NNPP ke yi na gudanar da zanga-zanga kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.
Ɗaliban sun bayyana goyon bayansu ga jam'iyyar All Progressive Congress (APC), tare da ɗan takararta Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, cewar rahoton PM News.
Da ya ke zantawa da manema labarai a cibiyar NUJ, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Yahaya Usman Kabo, ya yi kira ga jama'a da su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa Nasiru Gawuna ya yi nasara a kotun ƙoli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗaliban sun yabi ɓangaren shari'a
Usman ya yaba wa ɓangaren shari'a kan yadda suka yanke hukunci a ƙararrakin zaɓuɓɓukan 2023, inda ya ce hakan ya ƙara sabunta fatan ƴan Najeriya na samun ingantacciyar ƙasa.
A kalamansa:
"Ina so in bayyana wa jama’a cewa ɗaliban Kano ba su shiga duk wata zanga-zangar Kwankwasiyya ta NNPP ba ciki har da duk kokensu ga EU, AU, da ECOWAS."
"Wannan ba komai ba ne illa makircin da aka tsara da kuma nufinsu na kawo cikas ga zaman lafiya a jihar mu. Don haka muna Allah wadai da duk wani mummunan yunƙuri nasu da kuma ɗaukarsu a matsayin masu ɓata sunan jihar Kano da Najeriya gaba ɗaya."
"A ƙarshe ina amfani da wannan dama wajen kira ga ɗaliban mu da su cigaba da ba da jajircewa wajen nuna goyon baƴa ga Dakta Nasiru Yusuf Gawuna domin ya yi alkawarin inganta fannin Iliminmu, kuma muna da ƙwarin gwiwar cewa ba zai ci amanar mu ba."
Malaman Addinin Musulunci Sun Yi Wa Gawuna Addu'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu malaman addinin musulunci na ƙungiyoyi uku na Tijjaniyya, Izala da Ƙadiriyya sun yi addu'o'i na musamman ga Gawuna.
Malaman addinin musuluncin sun yi addu'o'in ne domin neman nasara ga ɗan takarar na APC a shari'ar gwamnan Kano da za a yi a kotun ƙoli.
Asali: Legit.ng