Kotun Koli: Jam’iyyun Adawa Sun Huro Wuta Sai An Tsige Abba, Aliyu da Wasu Gwamnoni

Kotun Koli: Jam’iyyun Adawa Sun Huro Wuta Sai An Tsige Abba, Aliyu da Wasu Gwamnoni

  • Alkalan kotun koli za su fara sauraron shari’ar da aka daukaka a kan zaben wasu gwamnonin jihohi
  • Wannan hukunci da za ayi ne zai kawo karshen shari’ar takarar gwamnan da aka yi a zaben na 2023
  • Jihohin da jam’iyyun adawa su ke harin karbe mulki sun hada da Kano da Filato da aka tsige gwamnoni

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ‘yan kwanakin nan, alkalan kotun koli za su zauna domin a yanke hukuncin shari’ar zaben gwamnonin jihohi.

Rahoton Daily Trust ya ce ana sauraron hukuncin babban kotun kasar a kan shari’ar jihohin Kano, Legas, Sokoto sai kuma Filato.

Kotun koli
Gwamnonin Filato, Kano da Sokoto suna Kotun koli Hoto: @KYusufAbba @HEAhmedAliyu @CalebMutfwan
Asali: Twitter

Legas

A ranar Talata, alkalai biyar a karkashin jagorancin Inyang Okoro su ka shirya yanke lokacin da za ayi hukunci a shari’ar gwamnan Legas.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar da ke neman tsige gwamnan APC, ta ba da dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan takaran LP, Bode Rhodes-Vivour da na PDP, Abdulazeez Adediran sun kalubalanci nasarar Babajide Sanwo-Olu a zaben Legas.

Filato

A game da shari’ar gwamnan Filato, tashar AIT ta ce an daga sauraron shari’ar daga Talatar nan zuwa ranar Talata, 9 ga watan Junairu 2024.

Sai zuwa sabuwar shekara Caleb Mutfwang da Nentawe Yilwatda za su san matsayarsu.

Sokoto

‘Dan takaran PDP a zaben gwamnan Sokoto a 2023, Saidu Umar Ubandoma ya daukaka kara a kotun koli domin a tsige Ahmad Aliyu.

Wani cikin mukarraban Sanatan Kudancin Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a Twitter, Shafiu TRT ya hango an tsige gwamna Aliyu.

Za a tsige gwamnan Sokoto?

Da Legit tayi magana da Nafiu Muhammad Lema, ya shaida mata cewa suna fatan kotun koli za ta duba kararsu, ta tunbuke gwamnan.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Kotun koli ta tsaida ranar sauraron shari’ar zaben Gwamnan Kano

Mai taimakawa ‘dan takaran na PDP a zaben bana, ya ce sun roki a tsige Aliyu saboda zargin badakalar takardun mataimakin gwamna.

Idan haka ba ta samu ba, Nafiu Lema ya fada mana akalla PDP tana so alkalan kotun koli su umarci INEC ta sake zabe a wasu rumfunan jihar.

Kano

A makon nan aka samu labari kotun koli ta sa rana domin a fara zama a game da shari’ar zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a 2023.

Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna za su san matsayarsu yayin da kotun koli ta tsaida Alhamis dinnan a matsayin ranar yin zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng