"Dalilin da Ya Sa Na Kulla Yarjejeniya 8 da Wike", Gwamna Fubara Ya Magantu

"Dalilin da Ya Sa Na Kulla Yarjejeniya 8 da Wike", Gwamna Fubara Ya Magantu

  • Gwamna Fubara ya yi magana a karon farko bayan ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsa da Nyesom Wike
  • Gwamnan na jihar Rivers ya bayyana cewa babu farashin da za a biya wanda ya wuce ƙima domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya
  • Shugaba Tinubu ne dai ya shiga tsakani a rikicin siyasa na Rivers inda ya jagoranci cimma yarjejeniya takwas a tsakanin ɓangarorin biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa babu wani farashi wanda za a biya da ya wuce ƙima domin zaman lafiya a jihar.

Jaridar The Nation ta ce Fubara ya bayyana kudirinsa na tabbatar da zaman lafiya a jihar da tsakanin al’ummarta domin samar da cigaba.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan abu 1

Fubara ya magantu kan sulhu da Wike
Gwamna Fubara ya bayyana dalilin yin sulhu da Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Wannan alƙawarin dai na nuni ne ga yarjejeniyar Abuja, inda shi da sauran masu ruwa da tsaki suka ƙulla yarjejeniya takwas domin kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata, 19 ga watan Disamba, a wajen taron yaye ɗalibai karo na uku na jami’ar PAMO da ke garin Iriebe a ƙaramar hukumar Obio-Akpor.

Gwamna Fubara ya magantu kan sulhu da Wike

"Babu wani farashi da zai yi yawa da za a biya domin tabbatar da zaman lafiya." A cewarsa.

Fubara ya tabbatar da cewa a shirye yake ya cigaba da yin duk abin da ya dace wanda zai tabbatar da zaman lafiya.

Ya kuma ba da tabbacin cewa samar da ingantaccen tsarin ilimi da ayyukan kiwon lafiyar jama'a masu rahusa sun kasance abubuwa biyu masu muhimmanci a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan Arewa ya sa labule da babban hafsan tsaro na ƙasa kan muhimmin abu 1

PDP Ta Yi Watsi da Yarjejeniyar Wike da Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ƙasa ta yi fatali da yarjejeniyar da Shugaba Tinubu ya cimmawa tsakanin Gwamna Siminlayi Fubara na jihar Rivers da Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja.

Jam'iyyar dai ta bayyana wannan matsayar ne bayan ta kammala.wani taron gaggawa da ta kira kan rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar ta Rivers mai arziƙin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng