Zai Kawo Matsala: Yanzu ne Lokacin da Shugabanni Za Su Kora Wike Daga PDP Inji Hadimin Atiku

Zai Kawo Matsala: Yanzu ne Lokacin da Shugabanni Za Su Kora Wike Daga PDP Inji Hadimin Atiku

  • A wani babatunsa a dandalin Twitter, Demola Rewaju ya sake kawo shawarar ayi waje da Nyesom Wike daga PDP
  • Matashin ‘dan siyasa ya ce lokacin korar Ministan harkokin na Abuja ya yi saboda ya hada-kai da gwamnatin APC
  • Hadimin Atiku Abubakar ya ce akwai bambancin gwamnatin hadakar Olusegun Obasanjo da ta Bola Tinubu a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Demola Rewaju ya sake yin kira da a fatattaki Nyesom Wike daga jam’iyyar hamayya ta PDP saboda ya bi gwamnatin APC.

A wani jawabi da ya yi a shafin X (Twitter), Demola Rewaju ya nanata cewa babu dalilin cigaba da zama rumfa guda da Nyesom Wike.

WIke da Tinubu
Nyesom Wike ya bi Bola Tinubu Hoto; Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Nyesom Wike zai zama matsala a PDP?

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan abu 1

‘Dan siyasar ya zargi Ministan na Abuja da kawowa PDP cikas duk da yana cikin ‘ya ‘yanta, yake cewa ya gurbata gwamnonin hamayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimakawa Atiku Abubakar din wajen dabarun sadarwa ya ce burin Nyesom Wike shi ne ya rugurguza jam’iyyar PDP a zaben 2027.

Korafin da ake yi a kan Nyesom Wike

"Majalisar NWC ta kira taron NEC sai majalisar kolin jam’iyya (ta PDP) ta yanke matakin da za a dauka daga nan.
Dabarar Wike na ba Bola Tinubu damar zarcewa shi ne ya sa PDP ta tsaida ‘dan takara daga Kudu ya tunkari Tinubu.
Ya san cewa Arewa za ta gwammace ta goyi bayan Tinubu a kan wani shugaban kasa daga kudu ya yi shekaru takwas."

- Demola Rewaju

Rikicin Wike v Simi Fubara a PDP

Rewaju ya yi wadannan maganganu a Twitter ne da ya fahimci an yi zama a Aso Rock domin a sasanta Nyesom Wike da Simi Fubara.

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

Matashin ‘dan siyasar ya ji haushin ganin yadda wanda ake yi wa kallon jigo a PDP zai kai karar gwamnansu a gaban gwamnatin APC.

Babu dalilin korar mutum daga PDP haka kurum amma Rewaju ya ce dole a dauki mataki kan duk wanda ya ci amanar jam’iyyarsa.

...PDP ta kira taron gaggawa

Shugabannin PDP sun shiga taron gaggawa a Abuja kan rikicin jihar Ribas, rahoto ya nuna jam'iyyar ba ta gamsu da yarjejeniyar da aka yi ba.

Bola Tinubu ya nemi sulhunta Ministansa na Abuja da kuma Gwamna Simi Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng