Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matsayarta Kan Yarjejeniya 8 da Tinubu Ya Cimmawa Tsakanin Wike da Fubara

Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matsayarta Kan Yarjejeniya 8 da Tinubu Ya Cimmawa Tsakanin Wike da Fubara

  • Jam’iyyar PDP ta ce babu wani sassauci ga ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 25 da suka sauya sheƙa zuwa APC
  • Jam’iyyar ta ce ƴan majalisar da ke biyayya ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike su shirya wani sabon zabe domin sun rasa kujerunsu
  • Wannan matsayar ta sha bamban da yarjejeniya takwas da Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Sim Fubara da Wike suka amince da su a ranar Litinin 18 ga watan Disamba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan yarjeniyoyi takwas da shugaban kasa Bola Tinubu ya cimmawa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Jam'iyyar adawar ta ce babu wani sassauci ga tsofaffin ƴan majalisar dokokin jihar Rivers su 25, waɗanda suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan abu 1

PDP ta yi fatali da yarjejeniyar da aka cimma kan rikicin Rivers
Jam'iyyar PDP ta yi watsi da yarjejeniyar da aka cimma kan rikicin Wike da Gwamna Fubara Hoto: @govWike, @OfficialPDPNg, @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Jam’iyyar ta yanke wannan shawarar ne a ƙarshen taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar kan rikicin siyasar jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum ya fitar a ranar Talata, 19 ga watan Disamba, ta shafin PDP na X (wanda aka fi sani da Twitter) @OfficialPDPNig.

Meyasa jam'iyyar PDP ta ƙi amincewa da yarjejeniyar?

Damagum ya dage kan cewa ƴan majalisar sun rasa kujerunsu kuma zaɓin da ya rage shi ne su sake tsayawa takara a duk wata jam’iyyar siyasar da suke so.

Jam’iyyar ta ce babu wata ɓaraka a jam’iyyar PDP a kasa ko a wani mataki da zai sanya ƴan majalisar su sauya sheƙa zuwa APC.

Ƴan Siyasar da Suka Sa Hannu a Yarjejeniyar Wike da Fubara

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin yan siyasan da suka sanya hannu a yarjejeniya kawo karshen rikicin Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai manyan ƴan siyasa da suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da Shugaba Tinubu ya cimmawa tsakanin Wike da Gwamna Fubara na jihar Rivers.

An cimma yarjejeniyar ne domin kawo ƙarshen rikicin siyasar da ake yi a jihar ta Rivers mai arziƙin man fetur. Nuhu Ribadu da kakakin majalisar dokokin jihar na daga cikin waɗanda suka sa hannu a yarjejeniyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel