Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar da Ke Neman Tsige Gwamnan APC, Ta Ba da Dalilai

Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar da Ke Neman Tsige Gwamnan APC, Ta Ba da Dalilai

  • A yau Talata ce Kotun Koli ta zauna kan shari'ar zaben gwamnan jihar Legas da ake tababa a kai
  • Kotun ta tanadi hukuncin ne a yau Talata 19 ga watan Disamba inda 'yan takarar jam'iyyun PDP da LP ke kalubalantar zaben
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a, John Okoro ya bayyana wa masu karar cewa zai sanar da su lokacin da shari'ar ta kammala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Legas.

Kotun ta tanadi hukunci a yau Talata 19 ga watan Disamba inda 'yan takarar jam'iyyun PDP da LP ke kalubalantar zaben.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: 'Yan sanda sun cafke dalibin jami'ar ATBU da bindiga, an tura shi sashen CID

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC
Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Legas. Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Azeez Adediran, Gbadebo Rhodes-Vivour.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Legas?

Dan takarar jam'iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour da takwaransa na PDP, Azeez Adediran na kalubalantar zaben kan tafka magudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan takarar sun daukaka karar ce bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara da aka yanke kan shari'ar zaben da aka gudanar a watan Maris, cewar The Nation.

Gamayyar alkalan guda biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a, John Okoro ya bayyana wa masu karar cewa zai sanar da su lokacin da shari'ar ta kammala.

Wane sanarwa hukumar zabe ta yi a baya?

Mataimakin gwamnan jihar, Femi Hamzat da Sakataren Gwamnatin jihar da kuma sauran mukarraban gwamnatin Legas sun halarci zaman kotun, cewar Tori News.

Gwamna Sanwo-Olu ya yi nasara ne a zaben bayan samun takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Tun farko, Hukumar zabe ta ayyana Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben yayin da dan takarar jam'iyyar LP ya kasance na biyu a zaben.

Kara karanta wannan

Kotu ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar adamawa, ta ba da kwararan dalillai

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Legas

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Legas da ake yi.

Kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar APC, Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe gwamnan jihar.

Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafe-korafen 'yan takarar jam'iyyun PDP da LP kan kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.