Yan Najeriya Sun Fusata Yayin da Shugaba Tinubu Ya Umarci Gwamnan PDP Ya Canza Kasafin 2024
- Tsoma bakin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a rikicin siyasar jihar Ribas ya bar baya da ƙura a kafafen sada zumunta
- Wasu ƴan Najeriya sun nuna damuwarsu bisa yadda Gwamna Fubara ya aminta da yarjejeniyar da aka cimma a Villa da Wike
- Tinubu ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara, Nyesom Wike, Peter Odili da wasu masu ruwa da tsaki a Villa, kuma an warware rikicin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - An umarci Gwamna Siminalayi Fubara ya koma majalisar dokokin jihar Ribas ya sake gabatar da kasafin kuɗin 2024 a gaban dukkan mambobin majalisar.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wannan na ɗaya daga cikin yarjejeniyar da aka cimmawa a zaman sulhu da sauran masu ruwa da tsaki a Aso Villa ranar Litinin.
Bayan haka kuma gwamnan da sauran muƙarrabansa sun amince za su janye dukkan ƙararrakin da suka kai gaban kotu dangane da danbarwan siyasar Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci zaman neman masalaha a fadarsa da ke Abuja, kuma kowane ɓangare ya rattaɓa hannu a kan yarjejeniya 8.
Martanin yan Najeriya kan umarnin Fubara ya sake gabatar da kasafin 2024
Sai dai umarnin da aka baiwa Gwamna Fubara ya canza gabatar da kasafin 2024 a majalisa bai yi wa da yawan Najeriya daɗi ba. Sun maida martani a soshiyal midiya.
Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a a manhajar X, wanda aka fi sani da Twitter.
@Kaimegalos ya ce:
"Shikenan an kwace Ribas."
@ElozonaVictor ya ce:7
"Gwamna mai ci! gaskiya wannan mutumin ya bani kunya."
@JosephOnuorah ya wallafa cewa:
"Sim Fubara ya yi babban kuskuren da zai ci shi, gaskiya ba shi da kwarewa gaba ɗaya. Shekaru huɗu kaɗai zai yi idan ya yi sa'a. Mutane irin Wike mulki kawai suka sani."
@adedeji_ishow ya ce:
"Rattaba hannu kan yarjejeniyar da Fubara ya yi ba yana nufin aiwatarwa bane, nan gaba komai zai fito fili."
Malami ya tsaya takarar gwamna a Edo
A wani rahoton kuma Wani malamin addinin kirista ya ayyana shiga tseren takarar gwamnan jihar Edo a zaɓe mai zuwa na shekarar 2024.
Rabaran Andrew Obinyan ya bayyana cewa al'ummar jihar da wasu ƴan Najeriya masu kishi ne suka matsa masa lamba ya fito takara.
Asali: Legit.ng