Tinubu Ya Fara Tunanin Ɗauko Tsohon Ministan Buhari Ya Maye Gurbin Lalong, Ya Gana da Jiga-Jigai 2
- Shugaba Tinubu ya gana da tsohon ministan yaɗa labarai da al'adu a gwamnatin Muhammadu Buhari, Lai Muhammed
- Rahotanni sun nuna cewa Bola Ahmed Tinubu ya kuma yi kus-kus da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari
- Lai Muhammed na ɗaya daga cikin ministocin Buhari da suka ja hankalin ƴan Najeriya musamman ma takin haramta Twitter
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fara neman shawarwari kan wanda ya kamata ya maye gurbin Simon Lalong a matsayin ministan kwadago da samar da ayyukan yi.
A rahoton Bussines Day, Shugaba Tinubu ya gana da Lai Muhammed, tsohon ministan yaɗa labarai da al'adu a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari.
Bayan haka, Shugaban kasar ya kuma gana da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa ganawar Tinubu da manyan ƙusoshin jam'iyyar APC ya maida hankali ne kan wanda zai maye gurbin Lalong.
Idan baku manta ba Simon Lalong, tsohon gwamnan jihar Filato ya yi murabus daga kujerar ministan kwadago da samar da ayyukan yi na tarayya.
Ya ɗauki wannan matakin ne bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar masa da kujerar Sanatan Filato ta kudu, bisa haka ya zaɓi komawa majalisar dattawa.
Lai Muhammaed na ɗaya daga cikin ministocin da suka haddasa ruɗani da kace-nace a mulkin Buhari kuma a lokuta da dama matasan Najeriya na mahawara a kansa a sohiyal midiya.
Lai ya haramta Twitter na tsawon lokaci
A lokacin da yake kan madafun iko, Lai Muhammad ya haramta amfani da Twitter daga ranar 2 ga watan Yuni, 2021 har zuwa ranar 11 ga watan Janairu, 2022.
Ministan ya ɗauki wannan matakin ne bayan manhajar Twittar ta goge rubutun Muhammadu Buhari kana ta dakatar da shafinsa na wani ɗan lokaci.
Wasu Tsageru Suka Kai Hari Hukumar Gwamnati a Abuja
A wani rahoton kuma Jami'an ma'aikatar birnin Abuja (FCTA) sun damƙe wasu tsageru bisa kai hari hukumar gudanarwa na birni ranar Litinin.
Waɗanda aka kama sun mamaye harabar hukumar da ke Wuse ne domin nuna fushi kan rushe musu gine-gine a wata Anguwa.
Asali: Legit.ng