APC Ta Yi Nasara Yayin da Kotu Ta Dakatar da INEC Kan Sake Zaben ’Yan Majalisu 27, Ta Tura Gargadi

APC Ta Yi Nasara Yayin da Kotu Ta Dakatar da INEC Kan Sake Zaben ’Yan Majalisu 27, Ta Tura Gargadi

  • Yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa a jihar Rivers, babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan dambarwar siyasa a jihar
  • Kotun ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC kan shirinta na gudanar da zabe a mazabun ‘yan Majalisun
  • Mai Shari’a, Donatus Okorowo shi ya ba da wannan umarni inda Premium Times ta samu kwafin a ranar Lahadi 17 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta dakatar da hukumar zabe ta INEC kan sake zaben ‘yan Majalisu a jihar Rivers.

‘Yan Majalisun guda 27 sun sauya shekar ce zuwa jam’iyyar APC daga PDP inda jam’yyar ta rusa zaben nasu a jihar.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fada mana: Shugaban tsagin Majalisar jihar PDP ya fadi dalilin watsewarsu zuwa APC

Kotu ta yi hukunci kan dakatar INEC kan sake zaben 'yan Majalisu
Kotu a Abuja ta dakatar da INEC kan sake zaben 'yan Majlisu a jihar Rivers. Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Mai Shari’a, Donatus Okorowo shi ya ba da wannan umarni inda Premium Times ta samu kwafin a ranar Lahadi 17 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasar jihar ke kara kamari tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.

Shugaban Majalisar jihar, Edison Ehie shi ya rusa zaben ‘yan Majalisun inda ya ayyana kujerunsu babu kowa, cewar Punch.

Yayin da Edison ke samun goyon baya daga Gwamna Fubara na jihar, shugaban tsagin Majalisar, Martins Chike da sauran ‘yan Majalisar na tare da Nyesom Wike.

Wane korafi 'yan Mjalisar su ke yi?

Bangaren ‘yan Majalisun da ke goyon bayan Nyesom Wike sun shigar da kara kotu kan wannan mataki da jam’iyyar PDP ta dauka a kansu.

Lauyan ‘yan Majalisun, Peter Onuh ya bukaci kotun ta dakatar da hukumar INEC da PDP da kuma Majalisar kan matakin da su ke son dauka.

Kara karanta wannan

Kotu ta raba gardama kan shari'ar da ke neman tsige dan Majalisar PDP, ta ba da dalilai

Har ila yau, Martins Chike ya bukaci kotun ta dakatar da hukumar DSS da Babban Sifetan ‘yan sanda daga tauye musu hakki, cewar Mind Viewers.

Mai Shari’a Okorowo ya dakatar da hukumar INEC game da sake zabe a mazabar ‘yan Majalisun da PDP ta rusa zabensu inda ta hana INEC daukar duk wani mataki kan haka.

Alkalin kotun har ila yau, ya dage ci gaba da sauraran karar zaben ranar 28 ga watan Disambar wannan shekara.

Shugaban tsagin Majalisar ya fadi dalilin barinsu PDP

A wani labarin, Shugaban tsagin Majalisar jihar Rivers, Martins Chike Amaewhule ya bayyana dalilin barinsu jam’iyyar PDP.

Chike ya ce Shugaba Tinubu ne ya ba su tabbaci kan haka tare da samar da abubuwan ci gaba a yankinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.