Rikicin Rivers: Jam'iyyar PDP Ta Yi Sabon Gargadi Ga Yan Majalisar da Suka Sauya Sheka
- Jam’iyyar PDP reshen jihar Rivers ta sake nanata cewa kujerun ƴan majalisar da ke goyon bayan Wike da suka sauya sheƙa babu kowa a kansu
- Wannan ya sabawa iƙirarin da ƴan majalisar suka yi na cewa duk abin da sauran ƴan majalisar biyar ke yi a wurinsu ya zama na banza
- PDP ta kuma yi watsi da iƙirarin ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa na cewa jam'iyyar na fama da rikicin cikin gida
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Port Harcourt, jihar Rivers - Jam'iyyar PDP a jihar Rivers ta bayyana cewa a hukumance babu kowa a kan kujerun ƴan majalisar da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar PDP a jihar Rivers, Sidney Tambari Gbara, ya jaddada cewa akwai buƙatar waɗannan ƴan majalisar su bi ƙa'idojin da doka ta tanada, yana mai jaddada cewa a halin yanzu kujerunsu babu kowa.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Gbara ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Dukkanin mu muna sane da abin da ke faruwa a jihar, kuma masu zargin cewa akwai rikici a PDP da ya kai su ga sauya sheƙa su tabbatar da hakan."
"Ban san inda matsalar take ba. Sun fi dacewa su bayyana idan akwai matsala a jam’iyyar ko babu."
"A game da batun ƴan majalisar da suka sauya sheƙa suna magana kan yawan ƴan majalisa da rashin yawan ƴan majalisa domin gudanar da ayyukan majalisa, waɗanda suka sauya sheka an bayyana kujerunsu babu kowa. Gaskiyar ita ce, dole ne jihar ta cigaba."
Ƴan majalisar sun saɓa doka
Hakazalika, kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar, Joseph Johnson, ya bayyana cewa ƴan majalisar sun samu kansu cikin son ƙa'idojin dokar da suka yi watsi da su.
A kalamansa:
"Dokar da kuka kasa bi ba za ta kare ku ba. Ƴan majalisa 27 da mutanen mazaɓunsu suka zaɓa, sun yanke shawarar su kaucewa nauyin da aka ɗora musu. Sun fice daga aikin da suke yi a ƙashin kansu, sun ce sun kammala. Sun ɗauki tutar APC. Sun yi wa PDP bankwana. Me suke yi a kotu?"
Wike Ya Gargadi Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa minista babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya aike da sabon gargaɗi ga Gwamna Fubara.
Ministan wanda yake takun saƙa da gwamnan na jihar Rivers, ya gargade shi da cewa bai kamata ya cire tsanin da ya yi amfani da shi wajen hawa sama ba.
Asali: Legit.ng