Rikicin Rivers: Wike Ya Aike da Muhimmin Gargadi Ga Gwamna Fubara
- Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya gargadi ƴan siyasa da kada su cire tsanin da suka hau suka samu manyan muƙamai
- Wike ya bayyana haka ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ya ɓarke tsakaninsa da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers
- Tsohon gwamnan na Rivers ya ƙaryata rahoton cewa rikicin da ya dabaibaye jihar mai arzikin man fetur faɗa ne na ƙabilanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Port Harcourt, jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi gargaɗi ga ƴan siyasa a jihar Rivers.
Wike ya ce bai kamata ƴan siyasa su cire tsanin da suka hau domin kaiwa ga matsayi na ɗaukaka ba, su ma su bar wa wasu su hau, cewar rahoton Channels tv.
Tsohon gwamnan na Rivers ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga basaraken gargajiya na Ogbaland, Nwachukwu Nnam-Obi III, wanda ya zo domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa a gidansa da ke Port Harcourt a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Kada ku cire tsanin da kuka yi amfani da shi wajen hawa sama. Lokacin da kuke saukowa, ta yiwu tsanin ba zai kasance a wurin ba."
"Kuma ku bar tsanin domin sauran mutane su ma za su iya hawa wannan tsanin."
Jaridar The Punch ta ce Wike ya tabbatarwa da basaraken cewa yana maraba da shawarwarin zaman lafiya kuma zai saurari shawararsa.
Wike ya musanta akwai ƙabilanci a rikicin Rivers
Ministan na babban birnin tarayya Abuja ya yi watsi da iƙirarin cewa rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar rikicin ƙabilanci ne.
A kalamansa:
"Ba mu yi zaɓe bisa ƙabilanci ba, amma sai don haɗin kan Rivers."
"Ba za mu taɓa kasancewa cikin tashin hankali ba, amma za mu goyi bayan zaman lafiya."
"Akwai dokoki a cikin ƙungiyar siyasar da ta samar da kai."
Gwamna Fubara Ya So Yin Murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya so yin murabus daga muƙaminsa na gwamna.
Tsohon kakakin ƙungiyar PANDEF ya bayyana cewa gwamnan ya so yin murabus ne saboda rikicinsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng