Gwamna Fintiri Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Yayin da Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci

Gwamna Fintiri Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Yayin da Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci

  • Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yi magana kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke kan zaɓensa
  • Gwamnan ya yi buƙaci magaoya bayansa da al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu yayin da kotun ke shirin yanke hukunci
  • Fintiri ya yi nuni da cewa yana da fatan cewa kotun ɗaukaka ƙarar za ta tabbatar da nasarar da mutanen jihar suka ba shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya buƙaci magoya bayansa da al’ummar jihar da kada su firgita saboda yana ganin ba za a ƙwace musu nasara ba.

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tsayar da ranar Litinin 18 ga watan Disamba, 2023 domin yanke hukunci kan ƙarar da Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC ta shigar akan Gwamna Fintiri.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Fitaccen wawakin siyasa ya yi magana kan hukuncin da Kotun Koli za ta yanke

Gwamna Fintiri ya yi magantu gab da hukuncin kotun daukaka kara
Gwamna Fintiri ya bayyana fatansa kan hukuncin kotun daukaka kara Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Fintiri wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren yaɗa labaransa Mista Humoashi Wonosiko a wata hira ta wayar tarho ya ce babu wani abin fargaba saboda sun yi imanin cewa kotun ɗaukaka ƙara za ta tabbatar da zaɓin da mutane suka yi, cewar rahoton Nigerian Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fintiri ya magantu kan hukuncin kotu

"Kamar yadda aka yanke hukunci a kotun zaɓe, a fili yake cewa Umaru Fintiri na PDP ne ya lashe zaɓen, muna da ƙwarin gwiwar cewa hukuncin kotun ɗaukaka kara za ta yanke zai ba mu nasara." A cewarsa.

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar Litinin 18 ga watan Disamba domin yanke hukunci bayan sauraron ƙarar da ƴar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani da jam'iyyarta suka shigar kan Gwamna Fintiri, INEC da PDP.

Kara karanta wannan

Wike ya shiga matsala yayin da ake zarginsa da aikata wani mummunan laifi

Hakazalika ƴar takarar gwamna ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a zaɓen gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023, Aishatu Dahiru Binani ta buƙaci magoya bayanta da su kwantar da hankula tare da jaddada cewa "na yi imani da cewa kotun ɗaukaka ƙara za ta soke nasarar PDP.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗan jam'iyyar PDP a jihar Adamawa, mai suna Malam Aliyu Umar, wanda ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa Gwamna Fintiri zai yi nasara a kotun.

Ya bayyana cewa a bayyane yake cewa ƴar takarar APC ba za ta yi nasara ba saboda yaɗda kotun zaɓe ta yi fatali da ƙararta.

"Na yi mamaki da ƙarar ta kai har zuwa kotun ɗaukaka ƙara domin a bayyane yake cewa Gwamna Fintiri ne ya ci zaɓe." A cewarsa.

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yanke Hukunci Kan Zaɓen Nasarawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Nasarawa.

Kotun ta warware hukuncin da kotun zaɓe ta yi na soke zaɓen Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng