Ohanaeze Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa Igbo Suka Ki Zabar Tinubu a Zaben 2023

Ohanaeze Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa Igbo Suka Ki Zabar Tinubu a Zaben 2023

  • Cif Emmanuel Iwuanyanwu ya bayyana cewa babu wata ɓaraka tsakanin Yarabawa da Igbo a Najeriya
  • Ya bayyana hakan ne a wata ziyarar ban girma da ya kai fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu a Iga Iduganran
  • Shugaban na Ohanaeze ya yi ishara da cewa tattaunawa a kan rabuwar da ke tsakanin Ndigbo da Yarbawa ta makara, yana mai cewa "yanzu ba za mu iya rabuwa ba"

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo na duniya, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, ya bayyana babban dalilin da ya sa ƴan ƙabilar Igbo ba su goyi bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, a ziyarar da ya kai wa Sarkin Legas, Rilwan Akiolu, a fadarsa, Iwuanyanwu ya ce ƴan ƙabilar Igbo ba su zaɓi Tinubu ba saboda an ce musu lokacin su ne.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da jakadun wasu kashe 3 a Aso Villa, ya buƙaci su yi manyan abubuwa 2

Ohanaeze ta fadi dalilin kin zabar Tinubu
A zaben 2023 Tinubu bai samu kuri'u daga Igbo ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa, yanzu ɗaukacin al’ummar Igbo sun ƙuduri aniyar marawa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu baya, inji rahoton jaridar Nigerian Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iwuanyanwu don haka ya roƙi Sarkin da ya sabunta dangantaka tsakanin Igbo da Yarbawa a jihar Legas.

Da yake mayar da martani, Oba Akiolu ya buƙaci Igbo dake Legas da su riƙa bin dokoki da tabbatar da bin ƙa’ida, cewar rahoton Vanguard.

Meyasa Igbo ba su zabi Tinubu ba?

Shugaban na Ohanaeze ya ce:

"A lokacin zaɓen, mu Igbo ba mu zaɓi Bola ba saboda an ce mana lokacin mu ne."
"Bola ya kyautata mana sosai lokacin yana gwamna. Ya kyautata ma Ndigbo. A lokacin zaɓen gwamna Igbo da ke Legas suka zo wurina, na ce su goyi bayan Gwamna Sanwo Olu."
"Amma shugaban Najeriya a yau shine Bola Tinubu, Ohanaeze ta yi alƙawarin goyon bayan ɗan uwanmu saboda cikin murna jam'iyyarsa ta APC ta tsayar da shi.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Matasa marasa aikin yi sun aike da sako mai muhimmanci ga ministar Tinubu

"Ya shiga zaɓe aka bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, mutane sun je kotu, kotun ta ce Tinubu ne ya ci zaɓe, sun je kotun ƙoli, kotun koli ta ce shi ne ya yi nasara."

Rigingimun Siyasar da Suka Daɗe

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai rigingimun siyasar da aka daɗe ana gwabzawa a tsakanin manyan ƴan siyasa a Najeriya.

Rigimar Kwankwaso da Ganduje, Bafarawa da Wamakko na daga cikin takun saƙar siyasa da aka daɗe ana yi a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng