Abba vs Gawuna: Kada Ku Cinnawa Najeriya Wuta Saboda Zaben Gwamnan Kano – Shugabannin Hausawa a Kudu

Abba vs Gawuna: Kada Ku Cinnawa Najeriya Wuta Saboda Zaben Gwamnan Kano – Shugabannin Hausawa a Kudu

  • Sarakunan Hausawa mazauna Kudu maso Yamma sun koka kan yadda abubuwa ke gudana yanzu haka a jihar Kano
  • Shugabannin arewan sun gargadi yan siyasa a cewa rikicin siyasar Kano na iya yaduwa sauran yankunan Najeriya
  • Sun yi kira ga yan siyasa da dattawan kasar a kan su yi amfani da hikima da hankali wajen shawo kan halin da ake ciki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Sarakunan Hausawa a Kudu maso Yamma sun gargadi shugabannin siyasa da kada su cinnawa Najeriya wuta saboda zaben gwamnan jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana fama da tashin hankali a Kano gabannin hukuncin da Kotun Koli za ta yanke a kan takaddamar zaben.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Fitaccen wawakin siyasa ya yi magana kan hukuncin da Kotun Koli za ta yanke

Abba da Gawuna
Abba vs Gawuna: Kada Ku Cinnawa Najeriya Wuta Saboda Zaben Gwamnan Kano – Shugabannin Hausawa a Kudu Hoto: Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A makon jiya ne manyan jam'iyyun siyasa biyu a jihar, NNPP da APC suka sake kulla yarjejeniyar zaman lafiya gabannin hukuncin karshe da kotu za ta yanke a shari'ar da ke kalubalantar zaben Gwamna Abba Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan jiya ne Kotun Daukaka Kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da tsige Gwamna Yusuf na NNPP sannan ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna dan takarar gwamnan APC a matsayin zababben gwamnan jihar.

A wani hukunci na bai daya da kwamitin kotun karkashin Mai shari'a Moore Adumein suka yanke, sun kori karar da gwamnan Kanon ya shigar na kalubalantar hukuncin kotun zabe da ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.

Sarakunan Hausawa a kudu sun shiga damuwa kan shari'ar zaben Kano

Sai dai kuma, shugabannin Hausawa a Kudu maso Yamma sun gana a Abeokuta, jihar Ogun, a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, inda suna nuna damuwa kan tashin hankalin da ke fitowa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Shoprite za su yi gaba, kamfanoni 22 na hanyar shigowa Najeriya da kudi domin kasuwanci

Shugabannin karkashin inuwar kungiyar Sarakunan Hausawa a Kudu maso Yammacin Najeriya sun bayyana ci gaban na Kano a matsayin mai firgitarwa.

Da yake karanto matsayar sarakunan, Sarkin Sagamu, Alhaji Inuwa Garba, ya yi kira ga shugabannin Najeriya da su yi amfani da iliminsu da hikimar siyasa wajen magance matsalar Kano don gudun barkewar rikici da annoba.

A cewarsa, duk wani rikici da ya taso daga Kano zai iya bazuwa a fadin Najeriya saboda kasancewarta a tsakiya da kuma tasirinta a siyasar Arewa da Najeriya; yadda Jihar Kano ke da rinjaye a fannin tattalin arziki a yankin Arewa da Najeriya baki daya.

Ya kuma bayyana cewa akwai kabilu daban-daban mazauna Kano musamman mutanen Kudu maso Yamma, wadanda galibinsu yan kasuwa ne da ma'aikata, kuma mutane na sane da abun da ke faruwa, rahoton Kano Focus.

Garba ya ce:

"A matsayinmu na dattawa kuma sarakunan gargajiya, mun damu musamman ganin yadda mutanen mu na Kudu maso Yamma masu aiki tukuru za su iya shiga tsaka mai wuya, tunda sun mallaki kadarori daban-daban kamar gidaje, shaguna da sauran sana’o’i da jarin jari.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Gwamnonin Arewa sun hadu a Kaduna, karin bayani kan abin da za su tattauna

“A gaskiya, muna kira ga manyan shugabanninmu da su yi amfani da iliminsu da hikimar siyasa wajen magance matsalar Kano domin gujewa tashin hankali da rikici.
"Ba wannan kawai ba, matsalar Kano za ta iya bazuwa zuwa sauran yankunan kasar nan cikin sauki kamar yadda ya faru a zamanin mulkin shugaban kasa Shagari inda matsalar ta samo asali daga durkushewar dimokuradiyya a yankin Kudu maso Yamma.
"Saboda haka, tare da la'akari da tsaron mutane, rayuka da dukiyoyinsu, muna fatan dattawa da shugabanni za su yi amfani da hikimar don ceto lamarin."

Ya ce shugabannin sun fito ne domin tabbatar da zaman lafiya da lumana a kasar.

Tsokaci kan shari'ar zaben Kano

A wani labarin, mun ji cewa wani masani mai sharhi kan harkokin siyasa, Segun Akinleye, ya yi tsokaci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano da ke gaban kotun ƙoli.

A cewarsa, abu ne mai matuƙar wahala a yanzu a iya hasashen wanda zai samu nasara a hukuncin da ake dako a kotun koli kan sahihin wanda ya lashe zaɓen Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng