Gwamnan PDP Ya Maida Zazzafan Martani Yayin da Ake Shirin Tsige Shi Daga Kan Mulki

Gwamnan PDP Ya Maida Zazzafan Martani Yayin da Ake Shirin Tsige Shi Daga Kan Mulki

  • Rigima tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da magabacinsa, Nyesom Wike, ta ƙara ƙamari a jihar mai arzikin man fetur
  • Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya sa kafar wando ɗaya da Gwamna Fubara na PDP
  • Legit Hausa ta tattaro cewa watanni bakwai da suka gaba, Wike da Fubara na ɗasawa kuma makusantan juna ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Yayin da ake tsaka da rikici tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Siminalayi Fubara, gwamnan jihar Ribas ya aike da saƙo ga ƴan Najeriya.

A yau Jumu'a, 15 ga watan Disamba, 2023, Gwamna Fubara ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kare muradan al'ummar jihar Ribas ta kowane hali.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗau zafi, ya umarci wasu kwamishinoni su yi murabus nan take

Ministan Abuja da Gwamna Fubara.
Fubara Ya Yi Magana Mai Zafi Yayin da Rikicinsa da Wike Ya Tsananta, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Fubara ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Tuwita a baya, ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya jaddada cewa zai kwatanta adalci

A faifan bidiyon mai tsawon dakiku 54, an ji gwamnan yana ɗaukar wa al'ummar jihar Ribas alƙawarin zai masu adalci.

Shugaba lamba ɗaya a jihar ya ce:

"Muna ƙara godiya ga mutanen Ribas bisa ɗumbin goyon da kuke bamu kuma ina mai tabbatar da cewa zamu iya bakin iyawarmu wajen kare martaba da mutuncin mutanen mu."
"Ba tare da duba matsayi ko girma ba, Gwamnatin mu zata tafi da kowa kuma ta san nauyin da ya rataya a wuyanta. Kunnuwa da idanun mu a buɗe suke wajen sauraron bukatar talakawanmu."
"Ba zamu baku kunya ba, zamu ɗora kan manufar adalci da daidaito ga kowa."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fara shirin tsige gwamna daga kan madafun iko kan abu 1 tal

Wannan kalamai na Gwamna Fubara na zuwa ne yayin da wasu kwamishinoni da ke goyon bayan Ministan Abuja suka yi murabus daga kan muƙamansu.

Gwamna Fubara ya bada sabon umarni

A wani rahoton na daban Gwamna Fubara na jihar Ribas ya umarci dukkan kwamishinonin da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya naɗa su miƙa takardun murabus.

Zuwa yanzu, kwamishinoni bakwai waɗanda ke goyon bayan tsohon gwamna Wike, sun yi murabus daga kan muƙamansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262