Wike vs Fubara: Muhimman Dalilai Uku da Ka Iya Sa a Tsige Gwamnan PDP Daga Kan Mulki

Wike vs Fubara: Muhimman Dalilai Uku da Ka Iya Sa a Tsige Gwamnan PDP Daga Kan Mulki

Rigingimun siyasar jihar Ribas na ci gaba da ɗaukar hankali tunda yan majalisa 27 da ke goyon bayan tsohon gwamna, Nyesom Wike, suka fice daga PDP zuwa APC.

Bayan haka Gwamna Siminalayi Fubara ya maida martani mai zafi kan wannan sauya sheƙa ta hanyar da mai yiwuwa ya rasa kujerarsa.

Ministan Abuja Wike da Gwamna Fubara.
Rivers: Muhimman Dalilai Uku da Zasu Sa a Tsige Gwamna Fubara a Yanzu Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Garin ceton kansa daga tsarin siyasar uban gida da kuma makarantar siyasar Wike, ministan Abuja, Gwamna Fubara ya yi abinda ka iya raba shi da gadon mulki.

Akwai wasu muhimman dalilai uku da ka iya jawo Gwamna Fubara ya rasa kujerarsa ta gwamna duba da yadda rikici tsakaninsa da Wike ke karuwa. Legit Hausa ta tattaro muku su kamar haka:

Rushe muhimmin ginin Peter Odili da buldoza

Rushe ginin zauren majalisar dokokin jihar Ribas da Gwamna Fubara ya yi ba zai yi wa mafi akasarin masu ruwa da tsaki daɗi ba saboda Peter Odili ne ya yi ginin na biliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fara shirin tsige gwamna daga kan madafun iko kan abu 1 tal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Odili ya shafe zangon mulki biyu a matsayin gwamnan jihar Ribas daga 1999 zuwa 2007. 'Yan siyasa da al'umma suna girmama shi.

Shi kansa Wike da wanda ya gabace shi, Rotimi Amaechi, duk suna girmama tsohon gwamna, Peter Odili.

Saboda haka rushe muhimmin aikin da ya yi yayin da yake raye ba zai masa daɗi ba. Odili yana da ta cewa a zamanin mulkin Amaechi da Wike.

Gwamna Fubara ya nuna bai cancanta a ba shi amanar mulki ba bayan ya fara takun saƙa da uban gidansa watanni shida kacal bayan hawa kan madafun iko.

Tasirin tsohon gwamnan ya zarce jihar Rivers domin Odili dai ya yi zamani da Shugaba Bola Tinubu kuma zai iya sa gwamnatin tarayya ta sa ƙafar wando ɗaya da Fubara.

Ƙarfin tisirin APC da Shugaba Tinubu

Sabanin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya kauda kansa lokacin da Gwamna Obaseki ya garƙame majalisar dokokin Edo na shekaru, Tinubu mutum ne ɗan jam'iyya.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tinubu ya yi kokarin sulhu tsakanin Wike da Fubara, APC ta yi karin haske

Bola Tinubu ya nuna haka a rikicin siyasar jihar Ondo, ya shiga tsakani ya sansanta komai a lokacin da abubuwa suka dagule saboda rashin lafiyar Gwamna Akeredolu.

A Ribas, APC na da kusan kaso 90 na yan majalisar dokokin jihar a hannu, hakan wata alama ce da ke nuna jam'iyyar zata iya kwace jihar idan aka tsige Fubara.

Mai yiwuwa gwamnan ya ɗebo ruwan dafa kansa ta hanyar rusa majalisar dokokin jihar Ribas, wanda masana harkokin siyasa suka ce barazana ce ga dimokuradiyya.

Ƙarar da ke gaban kotun ƙoli

Gwamna Fubara ya shiga wannan yaƙi ne duk da bai gama zama daidai a gadon mulkin Ribas ba domin kuwa ɗan takarar APC, Tonye Cole, na gaban kotun koli don kwato haƙkinsa.

Wike ya yi kokarin kare Fubara a kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara amma da yiwuwar ba zai sake maimaita haka ba a kotun koli.

Kara karanta wannan

Duk da alaka mai tsami a tsakani, gwamnan PDP ya taya Wike murna, ya tura masa sako mai jan hankali

Haka nan kuma Wike ka iya haɗewa da Cole wajen tsige Fubara a kotun koli kuma ɗan takarar APC zai iya barin tsarin Amaechi ya koma wurin Wike.

Abu 2 da kan iya yanke hukunci shari'ar Kano

A wani rahoton na daban Wani masani mai sharhi kan harkokin siyasa, Segun Akinleye, ya yi tsokaci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano da ke gaban kotun ƙoli.

A cewarsa, abu ne mai matuƙar wahala a yanzu a iya hasashen wanda zai samu nasara a hukuncin da ake dako a kotun koli kan sahihin wanda ya lashe zaɓen Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262