
Latest







Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa rundunar dojoji sun yi kwanton bauna inda suka hallaka Ibrahim Kaboni da wasu ‘yan bindiga takwas a garin Tsafe da ke Zamfara.

Hoton da ake yaɗawa na Rabiu Kwankwaso sanye da hula mai ɗauke da tamabarin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba gaskiya ba ne, kirkirarsa aka yi.

Hajiya Ummu Gada ta koma APC tare da wasu mambobin PDP a Sokoto, tana zargin PDP da rashin adalci da kuma yaba wa ayyukan Gwamna Ahmed Aliyu a jihar.

Shugaban APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya ce kofar jam'iyyar a bude take ga kowa, musamman ga masu kishin kasa da ci gaba inda ya yi gargadi da gindaya sharuda.

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ga laifin masu cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba shi da amfanin komai wajen ciyar da shiyyar Arewa gaba.

Wasu mutane dauke da manyan makamai sun kutsa kasuwar garin Faruruwa da ke karamar hukumar Shanono, inda suka hallaka wasu, tare da garkuwa da mutane.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani mahaifi da kishiya kan daure dansu mai shekaru 7 bisa zargin daukar biskit a shagon mahaifin. An yanke kafafun yaron.

Mataimakin shugaban kasa, Shettima ya kaddamar da kwamitin kirkire-kirkire domin rage shigo da kaya da 50%, da gina tattalin arziki mai dogaro da fasaha a Najeriya.

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta karyata raɗe-raɗin da ke yawo cewa motar ayarin matar shugaban kasa ta kaɗe wata yarinya har ta mutu a jihar Ondo.
Masu zafi
Samu kari