Bayanai Sun Fito Kan Haduwar Kwankwaso da Jagororin NNPP Kafin Zaman Kotun Koli
- Rabiu Musa Kwankwaso ya zauna da wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya da na majalisar dattawa a karkashin NNPP
- Sanata Abdulrahman Sumaila mai wakiltar Kudancin Kano yana cikin wadanda su ka kebe da jagoran jam’iyyar NNPP
- Kwankwaso ya tattauna da Ali Sani Madaki, Abdulmumin Jibrin da Tijjani Jobe domin bunkasa tafiyar Kwankwasiyya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Jagora a NNPP kuma ‘dan takaran shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso. yana kokarin ganin jam’iyyarsu ta kara karfi.
A ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba 2023, jawabi ya fito cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zama da wasu manya a NNPP.
Hadimin ‘dan takaran shugaban Najeriyan, Saifullahi Hassan ya tabbatar da haka a shafukansa na Twitter da Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso ya zauna da 'yan NNPP
Malam Saifullahi Hassan ya ce Madugun na Kwankwasiyya ya yi zama da Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya na NNPP.
Makasudin zaman su shi ne ganin yadda za a karfafa tafiyar jam’iyya mai kayan dadi a matakin jihar Kano da kuma fadin Najeriya.
'Yan majalisar wakilai sun gana da Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso ya sa labule ne da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila da wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga Kano.
‘Yan majalisar tarayyan su ne: Hon. Ali Sani Madakin Gini, Hon. Abdulmumin Jibrin PhD da kuma Hon. Abdulkadir Tijjani Jobe.
‘Yan majalisar masu wakiltar Dala, Kiru/Bebeji, Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado suna cikin wadanda ake ji da su a tafiyar NNPP.
'Yan majalisa sun yi kus-kus da Kwankwaso
Kafin nan, Sanata Kwankwaso ya hadu da kusan daukacin ‘yan majalisar wakilai da na majalisar dattawa da ke karkashin NNPP.
Sanarwar ta ce an yi wannan zama ne a gidan Kwankwaso da ke Abuja inda Kawu Sumaila da Hon. Jibrin su ka jagoranci tawagar.
Wike ya tsaya a PDP ko ya shigo APC?
Idan aka koma siyasar Ribas, an ji labari jam’iyyar APC tayi amfani da rigimar Nyesom Wike da Simi Fubara domin karya PDP.
Tony Okocha ya fadawa Ministan Abuja cewa da zarar ya bar PDP mai adawa, za a mallaka masa shugabancin APC a jihar Ribas.
Asali: Legit.ng