Dan Takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a PDP Ya Jefar da Lema Ya Koma APC, Ya Fadi Dalilai
- Dan takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya a jam'iyyar PDP, Usman Ibrahim ya yi watsi da lema inda ya koma APC
- Dan takarar wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya sauya shekar ce a jiya Laraba 13 ga watan Disamba
- Ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a yankin Kaduna ta Tsakiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Jigon jami'yyar PDP a jihar Kaduna, Usman Ibrahim ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Usman wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya yi takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya a PDP.
Yaushe jigon PDP ya koma APC a Kaduna?
Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar murabus da ya fitar a jiya Laraba 13 ga watan Disamba, cewar Daily Trust
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a yankin Kaduna ta Tsakiya.
Ya ce:
"Wannan mataki na zuwa ne bayan ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi bakwai da ke Kaduna ta Tsakiya."
Mene dalilin komawar jigon PDP zuwa APC?
Ya kara da cewa:
"Na koma APC ne daga PDP saboda kawo abubuwan more rayuwa ga mazabar Kaduna ta Tsakiya da ma jihar Kaduna."
Jigon PDP ya ce ya samu kwarin gwiwa daga wadanda ya ke tare da su a Majalisar Tarayya da masu rike da manyan mukamai a Gwamnatin Tarayya.
Usman ya ce babban abin da ya dace idan ya na kishin Kaduna shi ne hada hannu da Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, cewar Channels TV.
An ga tashin hankali bayan gini ya ruguje kan mata da jaririnta mai kwanaki 9, mijin ya shiga yanayi
Jigon PDP ya koma APC a Ebonyi
A wani labarin, jigon jam'iyyar PDP a jihar Ebonyi, Odefa Obasi Odefa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Obasi shi ne tsohon mataimakin kakakin Majalisar jihar wanda ya wakilci mazabar Onicha ta Gabas a jihar.
Jam'iyyar APC a a Najeriya na ci gaba da karbar 'yan siyasa da dama daga jam'iyyun adawa zuwa jami'yyar tun bayan zabe.
Asali: Legit.ng