Ganduje Ya Yi Babban Kamu Bayan Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisa Ya Watsar da PDP Zuwa APC
- Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Ebonyi bayan jigon jam'iyyar PDP ya watsar da ita
- Odefa Obasi Odefa wanda tsohon mataimakin kakakin Majalisar jihar ce ya sauya sheka da wasu mutane 500 daga mazabar Onicha ta Gabas
- Yayin martaninshi, Gwamna Nwifuru ya ce kofar jami'yyar APC a bude ta ke a ko wane lokaci don masu shiga jam'iyyar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi - Jigon jami'yyar PDP a jihar Ebonyi, Odefa Obasi Odefa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Odefa wanda tsohon mataimakin kakakin Majalisar jihar ce ya sauya shekar ce da magoya bayansa 500.
Yaushe Odefa ya koma APC a Ebonyi?
Obasi ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara wurin Gwamna Ogbonnaya Nwifuru gidan gwamnatin jihar, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar ce saboda tallafa wa gwamnan a kokarinsa na bunkasa jihar.
Ya ce ya gane cewa Nwifuru ya na da kyakkyawar manufa a zuciyarsa na kawo sauyi a jihar, cewar Daily Post.
Wane martani gwamnan Ebonyi ya yi kan sauya shekar?
Yayin martaninshi, Gwamna Nwifuru ya ce kofar jami'yyar APC a bude ta ke a ko wane lokaci don masu shiga jam'iyyar musamman ma su manufa mai kyau.
Gwamnan ya kuma ba su tabbacin cewa da su da tsaffin 'yan jam'iyyar duka daya su ke a wurinsu inda ya ce za a basu dama iri daya.
Odefa Obasi idan ba a manta ba ya wakilci mazabar Onicha ta Gabas a Majalisar jihar tun daga shekarar 2007 har zuwa 2023
Ganduje ya shiga ganawar gaggawa da 'yan Majalisar Ondo
A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya shiga ganawar gaggawa da 'yan Majalisar jihar Ondo.
Ganduje ya shiga ganawar ce don ci gaba da shawo kan matsalar da ke faruwa a jihar musamman tsakaninsu da mataimakin gwamnan jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ta rikici tun bayan fara rashin lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu a jihar.
Asali: Legit.ng