Jam'iyyar APC Ta Yi Sabon Ɗan Majalisa Bayan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara
- Majalisar dokokin jihar Legas ta rantsar da Age Suleiman a matsayin sabon mamba mai wakiltar mazaɓar Amuwo-Odofin
- Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya kori Olukayode Doherty na jam'iyyar Labour Party
- Yayin da yake masa maraba, kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, ya buƙaci ya haɗa kai da sauran abokan aikinsa kuma ya riƙa tuna mutanensa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Ɗan takarar APC a mazaɓar mamba mai wakiltar Amuwo-Odofin ta 2 a majalisar dokokin jihar Legas, Rauf Age-Suleiman, ya karbi rantsuwar kama aiki ranar Laraba.
Age-Suleiman ya zama sabon ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Amuwo-Odofin bayan rantsar da shi a gaban kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa da sauran mambobi.
Majalisa ta shaida ratsuwar kama aikin sabon ɗan majalisar na APC awanni gabanin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da ƙunshin kasafin kuɗin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bisa haka, Age Suleiman ya maye gurbin Olukayode Doherty na jam'iyyar Labour Party, wanda kwanan nan kotun ɗaukaka ƙara ta tsige shi daga kujerar, The Nation ta ruwaito.
Yayin yanke hukunci, kotun mai zama a Legas ta kuma ayyana ɗan takarar APC na mazaɓar a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓe a ranar 18 ga watan Maris.
'Ka haɗa kai da sauran ƴan majalisa'
Da yake masa maraba zuwa majalisar, shugaban majalisar dokokin jihar Legas, Obasa ya roƙe shi da ya haɗa kai da sauran mambobin majalisa kuma ya riƙa tuna mutanen da yake wakilta.
Haka nan kuma Mista Obasa ya taya mai girma gwamnan jihar Legas, jam'iyyar APC da ɗaukacin al'ummar mazaɓar Amuwo-Odofin murna bisa samun sabon wakili.
A cewarsa, bayan kama aikin sabon ɗan majalisar, yanzu jam'iyyar APC mai mulki tana da ƴan majalisa 39 jimulla a majalisar dokokin jihar Legas, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin ICPC da FCSC
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC), Musa Adamu a Aso Villa ranar Laraba
Bayan haka shugaban ya kuma baiwa sabon shugaban hukumar ma'aikata (FCSC) da mambobin hukumar 11 rantsuwar kama aiki.
Asali: Legit.ng