Gwamnatin Tinubu Ta Gano Wata Babbar Matsala da Buhari Ya Jawo Saboda Canjin Takardun Kuɗi

Gwamnatin Tinubu Ta Gano Wata Babbar Matsala da Buhari Ya Jawo Saboda Canjin Takardun Kuɗi

  • Gwammatin Najeriya ta ce canjin takardun Naira da CBN ya yi a lokacin kaka na cikin abinda suka kawo matsalar ƙarancin abinci
  • Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya ce canja kuɗi da rashin tsaro sun jefa manoma cikin fatara da talauci
  • 'Yan majalisar tarayya sun yi kira ga FG ta gaggauta shawo kan matsalar yunwa wacce rashin tsaro ya jefa mutane ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta koka kan yadda tsarin sauya fasalin Naira wanda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta aiwatar ya jefa manoma cikin mawuyacin hali.

Ministan noma, Abubakar Kyari.
Yadda Tsarin sauya fasalin Naira ya gurguntar da manoma, Ministan Noma Hoto: Abubakar Kyari
Asali: Facebook

Ministan noma da samar da wadataccen abinci, Abubakar Kyari, a ranar Litinin, ya ce tsarin canjin kudin da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi ya gurgunta kuɗin shigar manoma.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dira Kaduna kan kisan musulmai a bikin Maulidi, ya faɗi matsalar da aka samu tun farko

Daily Trust ta tattaro cewa CBN ya canja fasalin N200, N500 da N100 a ƙarshen shekarar 2022 kuma ya gindaya watan Fabrairu a matsayin wa'adin daina karɓan tsoffin kuɗi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kusan dai wannan tsari na canja kudi ya kawo cikas da taɓarɓarewa ga tattalin arziƙi sakamakon matsanancin karancin takardun kiɗi a hannun ƴan Najeriya.

Matsala biyu da suka kawo ƙarancin abinci a Najeriya

Da yake jawabi yayin da ya gurfana a gaban kwamitin noma na majalisar tarayya domin kare kasafin kuɗin ma'aikatarsa, Ministan ya yi magana kan ƙarancin abinci.

A cewarsa, wasu manyan dalilai ne suka haddasa barazanar ƙarancin abinci a ƙasar nan kamar matsalar tsaro da canja takardun naira da aka yi.

Kyari ya ce abubuwa da dama da suka hada da rashin tsaro da manufar sake fasalin kudin Naira sun jefa manoma cikin talauci da kunci, wanda ya zama barazana ga wadatar abinci.

Kara karanta wannan

Magidanci ya yi kokarin salwantar da ran matarsa kan abu 1

The Nation ta rahoto Ministan na cewa:

"Ƙuncin ƙarancin kuɗi da aka sha fama da shi sakamakon canza takardun Naira ya sa manoma siyar da kayayyakin su kamar kyauta saboda su rayu domin masu saye ba su samun kudin da zasu sayi amfanin gona."
"Tsarin canza kuɗin wanda aka aiwatar a lokacin kaka watau lokacin da amfanin gona ya zo, ya sa manoma sun shiga halin fatara da babu saboda ƙarancin Naira."

Bayan haka ne, ‘yan majalisar sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar yunwa wadda rashin tsaro ya haifar a ƙasar nan.

Jigon APC ya tsoma baki a rikicin Ribas

A wani rahoton Jigon APC a Oyo, Akin Akinwale, ya jero wasu batutuwa uku da suka faru gabanin mambobi 27 na majalisar dokokin Ribas su sauya sheƙa.

A cewarsa ƴan majalisar waɗanda aka gani a bidiyo suna rera waƙar Shugaba Tinubu sun koma APC kwana kaɗan bayan Wike ya yi irin haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel