Rikicin Siyasar Rivers: Jigon APC Ya Yi Wa Gwamna Fubara Wankin Babban Bargo

Rikicin Siyasar Rivers: Jigon APC Ya Yi Wa Gwamna Fubara Wankin Babban Bargo

  • Jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers ya yi tsokaci kan salon mulkin Gwamna Fubara
  • Tony Okocha ya bayyana cewa Gwamna Fubara ya kasa taɓuka komai bayan ya kwashe wata shida kan mulki
  • Okocha ya yi nuni da cewa Fubara ya kasa cika alƙawarin da ya ɗauka na cigaba daga inda tsohon Gwamna Wike ya tsaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers ta soki salon kamun ludayin gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara.

Jam'iyyar ta zargi gwamnan da nuna rashin ingantaccen shugabanci, rashin iya gudanar da mulki da kuma gaza cika alkawarin da ya ɗauka na tabbatar da nasarorin da tsohon Gwamna Wike ya samu, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da suka faru gabanin yan Majalisa 27 su sauya sheka daga PDP zuwa APC

Jigon APC ya caccaki Gwamna Fubara
Tony Okocha ya soki salon mulkin Gwamna Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Tony Okocha, shugaban kwamitin riƙo na jam'iyyar APC reshen Rivers ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ƴan majalisa 27 da ke biyayya ga Wike daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP zuwa APC a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okocha ya soki Gwamna Fubara

Tony Okocha wanda ya yi magana a wani shirin kai tsaye na gidan rediyon Infofm da ke Port Harcourt ya ce gwamnan ba shi da wani abin da zai iya nunawa bayan ya shafe watanni shida yana mulki, don haka ya bayyana gwamnatinsa da cewa ta gaza.

"Gwamnatin jihar Rivers ta mutu. Gwamna Siminalayi Fubara ya kauce daga tsari, wanda ya ce zai cigaba da ɗorawa a kai. Ya kauce ba domin yana da mafi kyawun tsari ba, sai domin baya da wani sabon abu."

Kara karanta wannan

Wike v Fubara: Asalin dalilin ‘Yan majalisan Ribas na dawowa APC Inji Jagororin Jam’iyya

Waɗannan ababen more rayuwan da muka sani waɗanda a dalilinsu jam'iyyar APC ta wancan lokacin ta karrama tsohon Gwamna Wike, duk sun tafi. Wane abu sabo a kayi a cikin wata shida?"

Okocha wanda shi ne wakilin jihar Rivers, a hukumar NDDC ya ƙara da cewa:

"A takaice, duk gwamnatin da ta yi kwana 100 a ofis kuma ba ta tsinana komai ba, wannan gwamnatin ta gaza."

Lauya Ya Magantu Kan Yan Majalisar da Suka Koma PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban lauya ya yi magana kan matsayar kujerun ƴan majalisar dokokin jihar Rivers na jam'iyyar PDP da suka koma APC.

Kalu Kalu ya bayyana cewa ƴan majalisar a bisa tsarin doka sun rasa kujerunsu bayan sun sauya sheƙa zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng