PDP vs APC: Tsohon Gwamnan Filato Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli

PDP vs APC: Tsohon Gwamnan Filato Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli

  • Tsohon gwamnan Filato ya yi bayani kan yadda Kotun Koli za ta yanke hukunci kan takaddamar zaben jihar
  • Fidelis Tapgun, jigon PDP, ya jaddada cewar jam’iyyarsa ba za ta tsira daga hukuncin Kotun Koli ba wanda ba zai banbanta da wanda kotun zabe da kotun daukaka kara suka yanke ba
  • A cewarsa, Caleb Mutfwang, da sauran yan majalisun da aka tsige sun rigada sun san matsalolin da ke kasa amma suka je suka yi takara duk da umurnin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Plateu - Awani al'amari mai ban mamaki, tsohon gwamnan jihar Filato, Fidelis Tapgun ya yi hasashen yadda hukuncin Kotun Koli za ta kasance a shari'ar Caleb Mutfwang.

Ku tuna cewa gwamnan jihar Filato Mutfwang ya garzaya Kotun Koli domin kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da na kotun zaben jihar da suka soke zabensa.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Fitaccen malamin addini ya yi sabon hasashe kan takaddamar zaben Kano

Jigon PDP a Filato ya ce jam'iyyarsa ba za ta yi nasara ba a Kotun Koli
PDP vs APC: Tsohon Gwamnan Filato Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Tapgun ya ce ya gargadi jam'iyyarsa kafin babban zaben 2023 kan hukuncin da kotu ta yanke a baya kan tsarin PDP amma suka yi watsi da gargadinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tsohon gwamnan, babu yadda za a yi PDP ta tsallake a Kotun Koli saboda Kotun daukaka kara ta tsige dukkan yan majalisun jiha da na tarayya da suka yi takara karkashin inuwar PDP kan cewa jam'iyyar bata da tsarin da za ta dauki nauyin yan takara a zabe.

Ya kuma ce Kotun Daukaka kara ta tsige Gwamna Muftwang kan wannan hujjar ne itama.

Daily Trust ta kuma rahoto cewa Tapgun ya shawarci Muftwang da ya yi murabus daga kujarersa na gwamna.

Kungiya ta magantu kan zaben Filato

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa wata kungiyar arewa mai suna 'Northern Initiative for Peace and Economic Development', ta bukaci Kotun Koli da ta jingine hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnan jihar Filato.

Kara karanta wannan

Shari'ar Kano: Lauya mazaunin Kano ya yi hasashen damar Abba Kabir a Kotun Koli

Abel Jilemsam, shugaban kungiyar, ya yi jawabi ga manema labarai a garin Jos, jihar Filato kwanan nan sannan ya bukaci Kotun Koli da ta mutunta zabin al'ummar Filato.

A cewarsa, hukuncin kotun daukaka kara da ya tsige Gwamna Mutfwang ya saba muradin al'ummar Filato, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng