Tsige Abba: Magoya bayan Kwankwaso sun shirya gagarumin abu 1 a kotun koli, NNPP ta yi bayani

Tsige Abba: Magoya bayan Kwankwaso sun shirya gagarumin abu 1 a kotun koli, NNPP ta yi bayani

  • Jam'iyyar NNPP ta musanta zargin cewa mambobinta da yan Kwankwasiyya sun shirya mamaye kotun koli da ofisoshin jakadancin ƙasashe
  • Shugaban NNPP na ƙasa, Abba Ali, ya ce zargin abun dariya ne domin jam'iyyar ta kasance mai bin doka da oda
  • Ya kuma bayyana ƙwarin guiwarsa kan ɓangaren shari'a yayin da ake dakon hukuncin kotun koli a shari'ar zaben Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi watsi da zargin cewa jam’iyyar da 'yan Kwankwasiyya na shirin mamaye kotun koli da ofisoshin jakadancin kasashen waje a Najeriya.

Jam'iyyar NNPP ta musanta zargin da ake mata.
Bamu da shirin mamaye kotun koli da ofishin jakadancin wasu ƙasashe, in ji NNPP Hoto: NNPP
Asali: UGC

Jam'iyyar NNPP ta bayyana zargin da ake mata da wani babban tuggu da bara gurbin tunani na wasu gamayyar ƙungiyoyin fararen hula, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

SDP ta yi maja da PDP, NNPP da sauransu don yakice Tinubu? Jam'iyyar adawa ta fadi gaskiya

Muƙaddashin shugaban NNPP na ƙasa, Abba Ali, shi ne ya musanta zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 8 ga watan Satumba, 2023, Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanasa ya ce:

"Zarge-zargen da kungiyoyin suka yi abin dariya ne, ya kuma nuna irin yadda ‘yan adawa a Jihar Kano za su je su kirkiro karya domin neman kwace mulki ta kowace hanya."
"APC ta san ba zata kai labari ba a kotun koli shiyasa ta koma ƙulla makirci, tsoratarwa, ƙarya da nufin girgiza mutane, shari'a da jami'an tsaro a kwace mulkin Kano wanda cikin sauki NNPP ta samu."

NNPP ta jaddada kwarin guiwa kan ɓangaren shari'a

Ali ya kuma bayyana cewa jam'iyyar NNPP na da kwarin guiwa da ɓangaren shari'a na ƙasa a matsayinsa na wurin tabbatar da adalci kuma gatan wanda ba shi da ƙarfi.

Kara karanta wannan

Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta

A cewarsa, NNPP jam'iyya ce mai bin doka da oda kuma zata jajirce iya ƙarfinta wajen ƙare hakkinta a sassan ƙasar nan, sannan ba zata lamurci duk wani yunƙuri na kawo cikas ba.

Abba Ali ya kara da cewa, "kuri'ar zabe abu ne mai matukar muhimmanci, kuma ba a tattaunawa ko siyarwa."

APC da NNPP sun jaddada yarjejeniyar zaman lafiya a Kano

A wani rahoton na daban kuma Manyan jam'iyyu biyu masu adawa da juna a jihar Kano, NNPP da APC sun sake sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Jam'iyyun biyu sun yi haka ne ranar Jumu'a domin tabbatar da zaman lafiya gabanin, lokacin da kuma bayan hukuncin kotun koli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262