Yanzun Nan: Lalong Ya Magantu Kan Barin Majalisar Tinubu Ko Komawa Majalisar Dattawa
- Minista Simon Lalong, na cikin tsaka mai wuya kan abu na gaba da ya kamata ya yi dangane da kujerarsa na sanata ko ci gaba da aikinsa na minista
- Hakan na zuwa ne bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara, ya ayyana Lalong a matsayin ainahin wanda ya lashe zaben sanatan Filato ta kudu
- A wata hira da aka yi da shi, Lalong ya nemi zabin Allah da goyon bayan jama'a yayin da yake tunanin yanke shawara mai mahimmanci da za ta daidaita makomar siyasarsa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Simon Lalong, ministan kwadago da daukar ma'aikata a gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi karin bayani dangane da mataki na gaba da zai dauka.
Tsohon gwamnan na jihar Filato ya nanata cewa a yanzu haka yana cikin rudani game da ko ya tsaya a matsayin minista a majalisar Tinubu ko kuma ya karbi kujerarsa a majalisar dattawa.
Ministan kwadagon ya bayyana cewa yana tsaka mai wuya kan lamarin, rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun zabe da ta ayyana Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Filato ta kudu.
Kwamitin mutum uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin Mai shari’a Elfrieda Williams-Dawodu ne ya yanke hukuncin a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba.
Sai dai kuma a wani bidiyo da ke yawo da tashar talbijin na yanar gizo ta saki, Lalong ya ce ya shiga rudani kuma ya gaza yanke shawarar ko ya karbi kujerarsa a majalisar dattawa ko ya ci gaba da mukamin minista.
A cikin bidiyon, ministan ya bukaci masu sauraronsa su yi masa addu’a domin ya yanke shawara mai kyau.
Simon Lalong na iya komawa majalisa
A wani labarin, mun kawo a baya cewa Simon Lalong, ministan kwadago da daukar ma'aikata, ya karbi takardar shaidar cin zabe a matsayin sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a majalisar dokokin tarayya.
Da farko Lalong, wanda ya yi gwamnan jihar Filato sau biyu, ya fadi zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, inda ya sha kaye a hannun Napoleon Bali na jam'iyyar PDP, kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana.
Asali: Legit.ng