Ministan Tinubu Ya Magantu Bayan Bore Na Yin Murabus da Ake Yi a Kansa, Ya Wofantar da Lamarin

Ministan Tinubu Ya Magantu Bayan Bore Na Yin Murabus da Ake Yi a Kansa, Ya Wofantar da Lamarin

  • Ministan birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi martani kan kiransa da yin murabus daga mukaminsa
  • Wike ya ce wannan ba yau ya fara gani ba kuma ya sani an biya su ne don yin wannan zanga-zangar inda ya ce dimukradiyya ce
  • Ministan ya bayyana haka ne a yau Alhamis 7 ga watan Disamba yayin kaddamar da wani shiri a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake zanga-zangar murabus din Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi martani kan kiran.

Wike ya ce kowa ya na damar yin haka ganin yadda ake cikin mulkin dimukradiyya.

Wike ya yi kakkausar suka kan masu neman ya yi murabus
Wike ya yi martani kan masu neman sai ya yi murabus. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Mene ya sa Wike martanin?

Wannan na zuwa ne bayan wasu 'yan asalin birnin Abuja sun yi zanga-zanga kan cewa sai Wike ya yi murabus daga kujerarshi.

Kara karanta wannan

Sabuwar zanga-zanga ta barke a Abuja kan kujerar Wike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bai kamata wani ya tsorata ba don kawai ana zanga-zangar cewa ya sauka a kujerarshi.

Ministan ya bayyana haka ne a yau Alhamis 7 ga watan Disamba yayin kaddamar da wani shiri a Abuja.

TVC News ta tattaro Wike na cewa:

"Jiya wani ya fadamin wai wasu sun fito su na zanga-zanga yayin da su ke daga kwalaye.
"Abu daya da ya kamata ku sani shi ne mu na mulkin dimukradiyya kuma kowa ya na iya nuna damuwarsa.
"Sai dai kuma dole mu yi abin da ya dace ga wannan birni, ba za mu ci gaba da yin abu daya ba kuma mu yi tsammanin sakamako."

Ministan ya ce a yanzu ana cikin wani yanayi dole a rinka daukar matakai masu tsauri don dakile matsalolin da ake samu, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi zanga zanga a Majalisa, sun ce Minista ya sauka bayan tono laifuffukansa

Mene Wike ya ce kan zanga-zangar?

Ya kara da cewa:

"Dole mu dauki matakai masu tsauri duk da halin da ake ciki wanda mutane za su ci moriya.
"Kada don wasu an biya su su na zanga-zanga ya tayar da hankali, tabbas an biya su kuma ta kare jiya."

Wike ya ce sun saba da ganin irin haka abin da ya kamata mutane su tambaye su shi ne mene su ka tsinana bayan damar da Shugaba Tinubu ya ba su.

An fara zanga-zangar murabus din Wike a Abuja

A wani labarin, wasu matasa 'yan asalin birnin Abuja sun fara zanga-zanga don Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi murabus.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da aka kirayi Ministan Tsaro, Badaru Abubakar ya yi murabus daga kujerarshi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.