Yan Bindiga Sun Sace Muhimman Takardun Ƙarar Zaben Gwamnan Arewa Da Ke Gaban Kotu

Yan Bindiga Sun Sace Muhimman Takardun Ƙarar Zaben Gwamnan Arewa Da Ke Gaban Kotu

  • Miyagun ƴan bindiga sun sace muhimman takardun da ke tattare da kararrakin zaben gwamnan jihar Kogi da aka kammala kwanan nan
  • Hukumar yan sanda ta ce maharan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne yayin da suka farmaki sakataren kotun saurarron karar zaben gwamna a Lokoja
  • A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 aka yi zaben gwamna a jihar Kogi, wanda ɗan takarar APC, Ododo ya samu nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kogi ta tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun farmaki sakataren kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar, David Umar Mike, a Lokoja.

Yan sanda sun tabbatar da sace takardun karar zabe a jihar Kogi.
Yanzun: Yan Bindiga Sun Sace Muhimman Takardun Ƙarar Zaben Gwamnan Arewa da ke Gaban Kotu Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Ta ce yayin harin na ranar Litinin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu muhimman takardun ƙarar da aka shigar kan zaɓen gwamnan Kogi wanda aka yi kwanan nan.

Kara karanta wannan

A Karshe, Jam'iyyar PDP ta fara ɗaukar matakan farfaɗowa daga bugun da ta sha a zaben 2023

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan, SP William Aya, shi ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Lokoja, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimman takardun da yan bindiga suka sace

Mai magana da yawun yan sandan ya ce maharan da suka farmaki sakataren kotun zaɓen, sun ƙwace dukkan takardun kararrakin da jam'iyyu biyar suka shigar.

A cewar hukumar yan sanda, takardun ƙorafe-ƙirafen da yan bindigan suka sace daga hannun Mista Mike sun haɗa da ƙarar jam'iyyun Action Alliance (AA), da Action People’s Party (APP).

Haka nan kuma maharan sun kwace takardun ƙararrakin Peoples Redemption Party (PRP) da kuma Social Democratic Party (SDP) daga hannun sakataren kotun.

Kakakin yan sandan Kogi ya ƙara da cewa bayan takardun kararrakin zaɓen, yan bindigan sun kuma sace litattafan ajiyar bayanai 2 da jaka mai ɗauke da kayan sakataren kotun.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka dasa bam a babbar jami'ar Najeriya, yan sanda sun yi bayani

Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa lamarin ya faru ne daf da ofishin babban bankin Najeriya (CBN) da misalin karfe 1:20 na ranar Litinin, cewar The Nation.

Sanata Barau ya buƙaci a yi bincike kan harin Kaduna

A wani rahoton na daban Sanata Barau Jibrin ya yi ta'aziyya ga dangin waɗanda harin bam ɗin sojoji ya shafa a kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kamar yadda Bola Tinubu ya bada umarni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262