Rigima Ta Ɓarke a APC, Majalisa Ta Dakatar 'Yan Majalisa Huɗu kan Muhimmin Abu 1
- Majalisar dokokin jihar Benuwai ta dakatar da mambobi guda huɗu kan faɗa da yan majalisa masu goyon bayan Gwamna Alia
- Wannan matakin ne zuwa ne yayin da rikicin cikin gida ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar
- Shugabannin APC da Gwamna Alia sun fara takun saƙa ne kan tsarin da ya zo da shi na raba mukaman gwamnati
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Rigingimun cikin gida da ke faruwa a jam'iyyar APC reshen jihar Benuwai ya fara jawo mata matsala a ranar Litinin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Majalisar dokokin jihar ta dakatar da ƴan majalisa hudu daga aiki biyo bayan kace-nace da ya haɗa su da wasu mambobin majalisa masu goyon bayan Gwamna Hyacinth Alia.
An tattaro cewa majalisar ta dakatar da yan majalisun ne bisa zargin yin zagon ƙasa ga zaman majalisar dokoki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan majalisa hudu da aka dakatar
Waɗanda majalisar ta dakatar sun haɗa da Solomon Gyila, mamba mai wakiltar mazaɓar Gwer ta yamma da Douglass Akya, mamba mai wakiltar mazaɓar Makurdi ta kudu.
Sauran su ne, Dyako Ashwa, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Konshisha da kuma na karshe, Anthony Agom, mai wakiltar mazaɓar Okpokwu a majalisar jihar Benuwai.
Rikicin da ya ɓarke a APC
Wannan dakatarwa na zuwa ne bayan dattawan APC a jihar sun yi taro a gidan gwamnati da ke Makurɗi domin kaɗa kuri'ar ƙwarin guiwa kan Gwamna Alia.
Sun yi haka ne duk da shugabannin jam'iyya na matakin jiha da ƙananan hukumomi sun fara juya wa gwamnan baya.
Dattawan APC karkashin tsohon shugaban majalisar dattawa, Ameh Ebute, da wasu da dama sun kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin warware duk wasu matsalolin cikin gida.
Tun a watan Yunin 2023 ne dai shugabannin jam'iyyar APC na jihar Benue da gwamnan ke takun-saka kan tsarin raba muƙamai, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Kungiyar Lauyoyi Ta Soki Hukuncin Tsige Abba Kabir Yusuf
A wani rahoton kuma Kungiyar matasan lauyoyin jihohin arewa 19 sun caccaki hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa hukuncin ya nuna rashin adalci ƙarara.
Asali: Legit.ng