Kano: APC Ta Bukaci Kowa Ya Bi Yarjejeniyar Zaman Lafiya Da Aka Sa Hannu
- Jam'iyyar APC ta zargi wasu shugabannin NNPP da saɓawa yarjejeniyar zaman lafiyam da suka sa wa hannu a hedkwatar yan sanda
- Mataimakin shugaban APC na Kano, Shehu Maigari, ya ce ya kamata 'yan sanda su ɗauki mataki domin a gabansu kowa ya sa hannu
- Ya ce mambobin APC za su ci gaba da zama lafiya da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tada zaune tsaye ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Shehu Maigari, ya bada tabbacin cewa za su ci gaba da bin yarjejeniyar zaman lafiya aka aka sa wa hannu a hukumar ‘yan sandan.
Maigari ya faɗi haka ne ranar Jumu'a yayin da yake amsa tambayoyin jaridar Leadership kan zanga-zangar da ƴan Kwankwasiyya ke yi.
Magoya bayan jam'iyyar NNPP mai kayan marmari na ci gaba da zanga-zanga domin nuna adawa da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi, mataimakin shugaban APC na Kano ya ce akwai zaman lafiya a jihar duba da yadda kowa ya maida hankali kan harkokinsa na yau da kullum.
APC ta zargi wasu da saɓa alkawarin zaman lafiya
Amma Maigari ya zargi wasu manyan mutane da saɓawa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattabawa hannu ta hanyar fitowa zanga-zanga.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da kada su tsorata da abin da wasu ‘yan tsiraru suka aikata, su kwantar da hankalinsu su jira hukuncin kotun koli.
Haka nan kuma ya roki hukumomin tsaro da ke kokarin tabbatar da bin doka da oda su tashi tsaye wajen tabbatar an bi yarjejeniyar kamar yadda kowa ya amince.
Shehu Maigari ya ce:
"Mutanen da ke Kano a halin yanzu sun san hakikanin halin da ake ciki, babu wani tashin hankali a jihar. Kowa yana gudanar da harkokinsa na yau da kullun."
“Babu tashin hankali a Kano a halin yanzu. Wasu mutane ne kawai masu son kai suke tsara abubuwan da ke faruwa mara daɗi."
"A makon jiya aka kira jam'iyyarmu APC da NNPP zuwa hedkwatar yan sanda muka sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, amma abun ban mamakin mutanen nan sun saɓa."
Ya bayyana cewa yan sanda na wurin lokacin da kowace jam'iyya ta sanya hannu, don haka ya rataya a wuyansu su tabbatar an samu tsaro, Daily Post ta tattaro.
APC zata kwace wasu jihohi a kudu - Akpabio
A wani rahoton kuma Sanata Godswill Akpabio ya yi ikirarin cewa APC mai mulki zata karɓi jihohin Kudu maso Kudu a zabe na gaba.
Shugaban majalisar dattawan ya ce ya kamata shiyyar ta gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu ta hanyar zaɓen jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng