Mataimakin Gwamnan APC Zai Rubuta Takardar Murabus Daga Muƙaminsa, Sahihan Bayanai Sun Fito

Mataimakin Gwamnan APC Zai Rubuta Takardar Murabus Daga Muƙaminsa, Sahihan Bayanai Sun Fito

  • Ana sa ran mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, zai rubuta takardar murabus da babu kwanan wata a jiki
  • Wannan na ɗaya daga cikin matsayar da aka cimma yayin zaman sulhu da Shugaba Tinubu a karshen makon nan
  • Kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Olamide Oladiji, ne ya tabbatar da haka yayin karanto rahoton zaman sulhun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, zai rubuta takardar murabus daga muƙaminsa ba tare da kwanan wata ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shugaban majalisar dokokin jihar, Olamide Oladiji, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi kan matsayar da suka cimma a zaman sulhu da shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya bankaɗo matsala kan yan ta'adda, ya buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa jihohi 6 a arewa

Mataimakin gwamnan jihar Ondo.
Sulhun Tinubu: Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Aiyedatiwa Zai Rubuta Takardar Murabus Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Ya ce suna dakon mataimakin gwamnan ya rattaba hannu kan takardar murabus mara kwanan wata a wani ɓangare na bin matakan sulhun da aka cimma a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnatin Ondo, Oladunni Odu, shugaban APC na jiha, Ade Adetimehin da Sanata Jimoh Ibrahim na cikin waɗanda suka halarci taron sulhun da Tinubu ya kira a karshen mako.

Yadda zaman majalisar dokokin Ondo ya gudana

An gabatar da rahoton sulhun ga mambobin majalisar dokokin a zamansu na jiya inda ‘yan majalisar suka ki aminta da matakin da wasu daga cikinsu suka dauka na bayyana Ayedatiwa a matsayin mukaddashin gwamna.

Kakakin majalisar, Olamide Oladiji, ne ya karanta yarjejeniyar da aka cimma a zaman sulhu da shugaban kasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa daga cikin matsayar da aka cimma akwai dakatar da yunkurin tsige mataimakin gwamna, janye kararrakin da ke gaban kotu, kowa ya rike matsayinsa a jam'iyya, gwamnati da majalisa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aike da muhimman saƙo ga majalisar dattawa kan kasafin kuɗin 2024 da zai gabatar

Aiyedatiwa ya ci gaba da zama a matsayin mataimakin gwamna ba muƙaddashin gwamna ba kuma ya ƙara nuna mubaya'a da biyayya ga Gwamna Rotimi Akeredolu.

Oladiji ya ƙara da cewa an nada kwamitin mutum uku wanda ya kunshi shi kansa, Odu da Adetimehin domin su sanya ido wajen tabbatar da an bi matakan sulhun.

Ya gargaɗi duk masu yunkurin ƙara rura wutar rabuwar kai saboda son kansu, yana mai cewa zasu fuskanci fushin doka idan ba su canja tunani ba.

Kakakin majalisar ya ce:

"A koda yaushe muna gudanar da ayyuka mu bisa tanadin doka duk da a baya an yi yunkurin shafa mana kashin kaji a matsayin da masu yin doka."

Rikicin Shugabanci Ya Barke a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka rikicin shugabanci .ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Kotun ta tsige kakakin majalisar da mataimakinsa, ta umarci INEC ta shirya sabon zabe a wasu rumfunan mazaɓu biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262