Gwamnan APC Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Gaskiyar Abinda Ya Shiga Tsakaninsa da Tsohon Gwamna

Gwamnan APC Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Gaskiyar Abinda Ya Shiga Tsakaninsa da Tsohon Gwamna

  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana abinda ya haɗa shi rigima da tsohon gwamnan da ya gada, Ibikunle Amosun
  • Abiodun, wanda ya samu nasarar tazarce a zaben watan Maris, ya ce saɓanin da ke tsakaninsa da Amosun sirri ne
  • Ya ce ba ya tunanin ko sun sasanta zai shafi tattalin arzikin jihar Ogun da kuma na ƙasar nan baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce matsalar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan da ya gabace shi, Ibikunle Amosun, “batu ne na kashin kai."

Gwamna Dapo Abiodun da magabacinsa.
Batun da ya hada ni rigima a Amosun na kashin kai ne, Gwamna Abiodun Hoto: channelstv
Asali: UGC

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a cikin shirin Sunday Politics.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-jigan APC da wasu da su ka caccaki Buhari kan jinginar da rubabbiyar gwamnati ga Tinubu

Abiodun ya bayyana cewa sulhu tsakaninsa da Amosun wani lamari ne na sirri kuma mai yiwuwa ba zai yi tasiri sosai ga cigaban tattalin arzikin jihar Ogun ko kasa baki daya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka tambaye shi ko ya samu damar sasantawa da tsohon gwamnan, Prince Abiodun ya ce, “Batun sulhu, na yi imani wadannan batutuwa ne da suka shafe ni na ƙashin kai."

"Bani da tabbacin ko sulhu tsakanina da magabaci na zai shafi ci gaban tattalin arzikin jihar Ogun ko kasar nan baki daya.”

Yadda rikici ya raba yan siyasar biyu

Amosun, wanda ya yi gwamnan jihar Ogun daga 2011 zuwa 2019 da kuma Abiodun wanda ya karbi mulki a shekarar 2019, sun dade suna takun saka tsakanin su.

Dukkan jiga-jigan siyasar biyu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne amma sun dare gida biyu, suna gudanar da harkokinsu daga tsagi daban-daban a jihar.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan ya sake fallasa yadda aka kai Najeriya gargara kafin zuwan Tinubu

Amosun, duk da kasancewarsa mamban jam’iyyar APC, ya goyi bayan dan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Biyi Otegbeye, a zaben gwamnan da aka yi a watan Maris, 2023.

Sai dai a zaben, Gwamna Abiodun ya samu nasarar tazarce karƙashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

A watan Mayu, Abiodun da Amosun sun yi musayar yawu da ɗora wa juna laifi kan wurin da Alhaji Aliko Ɗangote zai gina matatar man fetur.

Tinubu ya rantsar da mutane 8 da ya naɗa

Legit Hausa ta kawo labarin cewa Bola Tinubu ya rantsar da sabbin manyan sakatarori takwas da ya naɗa kwanan nan bayan sun tsallake tantancewa.

Jim kaɗan bayan haka, shugaban ƙasar ya jagoranci taron majalisar zartarwa (FEC) a fadarsa da ke Abuja ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262