Babban Lauya Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Nasarar Gwamnonin Kano da Plateau a Kotun Koli

Babban Lauya Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Nasarar Gwamnonin Kano da Plateau a Kotun Koli

  • Fitaccen lauya, Inibehe Effiong, ya yi magana a kan yiwuwar nasarar Gwamna Abba Yusuf na Kano da Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato a kotun ƙoli
  • Effiong ya ce gwamnonin biyu na da kyakyawar hujjar ɗaukaka ƙarar korar su da kotun ɗaukaka ƙara ta yi saboda dalilai na kafin zaɓe ne
  • A wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi, ya bayyana cewa a hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a baya, ta ce zama ɗan jam'iyya wani lamari ne na cikin gida wanda kotu ba ta da hurumin shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Inibehe Effiong, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf da Gwamna Caleb Muftwang na Jihohin Kano da Plateau suna da hujjojin ɗaukaka ƙara kan korar da aka yi musu a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Effiong ya ce dalilin korar gwamnonin na kafin zaɓe ne da kuma al’amuran da suka shafi jamiyya wanda kotu ba ta da hurumi a kai.

Effiong ya yi magana kan shari'ar gwamnonin Kano da Plateau
Effiong ya ce gwamnonin biyu na da dalilin zuwa kotun koli Hoto: Abba Yusuf/Inibehe Effiong/Caleb Muftwang
Asali: UGC

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen lauyan ya ce matakin da gwamnonin suka ɗauka na ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara yana da kyau duk da cewa ba zai iya hasashen sakamakon da za su samu a kotun ƙoli ba.

A kalamansa:

"Na yi amanna cewa batu ne wanda ya kamata kotun ƙoli ta yi duba a kansa saboda a hukunce-hukuncen baya kotun ɗaukaka ƙara ta ce zama ɗan jam'iyya abu ne na cikin gida na jam'iyyu kuma batu ne na kafin zaɓe wanda kotu ba ta da hurumi a kansa."

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Kano: Kotun daukaka kara ta bukaci lauyoyi su dawo da takardun hukuncin da ta yanke

"Ina son na ga yadda kotun ƙoli za ta kalli hakan. Na yi amanna cewa suna da dalilin ɗaukaka ƙara. Na ga hukuncin da aka yanke a Kano. Don haka a bari batun ya kai kotun ƙoli. Abu ne mai kyau da suka garzaya kotun ƙoli amma ba zan iya faɗin abin da zai faru ba, kawai zan iya ce muku suna da hujjar ɗaukaka ƙara."

Da yake magana a kan korar ƴan majalisun da aka yi na jam'iyyar PDP a jihar Plateau, Effiong ya ce kotun ɗaukaka ƙara ita ce matakin ƙarshe a shari'ar zaɓen ƴan majalisu.

Ya yi bayanin cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na korar ƴan majalisun PDP ba zai yi tasiri ba kan yadda kotun ƙoli za ta kalli shari'ar Gwamna Mutfwang.

NNPP Ta Magantu Kan Tsige Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kakakin jam'iyyar NNPP ya yi magana kan cece-kucen da ya biyo bayan takardun hukuncin ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Abba.

Ladipo Johnson, ya bayyana cewa za a magance cece-kucen da ake tafkawa dangane da CTC na hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan rikicin zaben gwamnan jihar Kano a kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel