Ministan Buhari Ya Bayyana Babban Kuskuren da Ya Yi Na Tura Sunan Wike a Matsayin Minista
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana mafi munin mataki da ya taba dauka a rayuwarsa
- Amaechi ya ce tura sunan Nyesom Wike a matsayin minista shi ne mafi munin shawara da ya taba karba
- Tsohon ministan ya bayyaana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ce shi ya san halin Wike tun a shekarun baya
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana dana sanin mika sunan Wike a matsayin Minsta.
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, an gano Amaechi na bayanin yayin ake rikicin siyasa a jihar Ribas.
Mene Amaechi ke cewa kan Wike?
Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin rikicin siyasa a jihar Ribas tsakanin Nyesom Wike da Gwamna Simi Fubara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike wanda ya tsayar da Fubara takarar gwamna ya zargi gwamnan da jawo matsalar da ke faruwa da kansa, Legit ta tattaro.
Amaechi ya ce:
“A siyasa a kwai wasu matakai da za ka yanke shawara a kansu, akwai kuma wadanda za ka tuntubi ‘yan siyasa.
“Lokacin da mu ka mika sunan minista, mun yanke shawarar mika sunan wani, an ki amincewa da shi, sai muka sake mika sunan wani inda aka amince da shi.
“Akwai abokin Wike, Chuma wanda kwamishina ne a gwamnati na, ya bukaci mu saka sunan Wike a mukamin minista zuwa ga tsohon Shugaba Jonathan.
Martanin Amaechi kan Wike?
Amaechi ya kara da cewa:
“idan ba don Chuma ba, ba zan saka sunanshi ba, duk yadda mutum ya yi da mukami shi ya sani, Wike ba ya cikin gwamnati na saboda na san bai cancanta ba ya kasance a gwamnati na.
“Idan Chuma bai zo da wannan shawara ba, ba zan yi ba, wannan ita ce mafi munin shawara da na taba karba a rayuwa saboda na san waye ne Wike.
“Mutane da dama sun yi mini magana kan tura sunan Wike, na yi dana sanin aikata haka a rayuwa ta.”
Wike ya magantu kan takara da Tinubu
Kun ji cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya magantu kan tsayawa takara da Shugaba Bola Tinubu.
Wike ya ce shi dan halak ne don haka ba ya bukatar tsayawa da Tinubu takara a zabe.
Asali: Legit.ng