Zargin Rashawa: Atoni Janar Na Kano Dederi Ya Shiga Matsala, An Nemi a Hukunta Shi
- An shigar da wani korafi na neman a binciki Haruna Isa Dederi, Atoni Janar na jihar Kano kuma kwamishinan shari'a
- Wannan bukatar ya biyo bayan zargin rashawa da Dederi ya yi wa alkalan kotun daukaka
- An tattaro cewa Dederi ya yi wannan zargi ne yayin wani shirin kai tsaye na Channels TV a makon jiya
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja – Kungiyar fafutukar tabbatar da adalci da shugabanci na gari (AJGG) ta nemi a gurfanar da Atoni Janar na jihar Kano kuma kwamishinan shari’a, Barista Haruna Isa Dederi.
Wannan kiran martani ne ga zargin rashawa da Dederi ya yi wa alkalan kotun daukaka kara.
A wata sanarwa da ya saki a Abuja a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, Mista Francis Nzeoke, jagoran kungiyar AJGG, ya jaddada bukatar kwamishinan ya bayar da cikakkun bayanai game da alkalan da ya zarga da karbar na goro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da ya yi
Dederi ya yi wadannan zarge-zargen ne a yayin da ya bayyana a shirin 'Sunrise Daily' na Channels TV a ranar Laraba da ta gabata.
Nzeoke ya yi karin haske kan yadda abubuwa suka faru a Kano, inda jami’an gwamnati suka dunga tozarta ma’aikatan shari’a a yayin da ake tsaka da shari’ar zabe.
Kungiyar ta ce:
"Muna kira ga hukumomi da su yi wa Dederi tambayoyi don ya gabatar da hujja kan dukkan zargin da ya yi a Channels TV. Idan ba zai iya ba toh ya kamata a kama shi sannan a hukunta shi.
"Mun damu da yadda abubuwa ke wakana a baya-bayan nan inda yan siyasa suka sha kaye a shari'arsu a kotu sannan su koma ga yin barazana ga alkalai. Ba abu ne mai kyau ga damokradiyyarmu da tsarin doka ba."
Kungiyar ta AJGG, tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sun yi alkawarin magantuwa kan duk wani yunkuri da yan siyasa ke yi na bata sunan alkalai ko ci masu zarafi.
Bugu da kari, kungiyar mai zaman kanta ta yi kira ga kungiyar lauyoyin Najeriya da ta dauki matakin ladabtarwa a kan mambobinta da aka samu da karya doka, rahoton Daily Post.
Abba da APC sun ja layi a Kano
A wani labarin, mun ji cewa gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya barranta da jami'yyar APC kan zanga-zangar da ake yi a jihar.
A jiya Laraba ce zanga-zanga ta barke bayan kotun daukaka kara ta saki takardun CTC da ya bai wa Abba Kabir nasara a kotu.
Asali: Legit.ng