Shugaba Tinubu Ya Gana da Ganduje da Gwamnoni Uku, Ya Musu Nasihar Yadda Zasu Ɗauki Talakawa
- Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan Kogi, zababbun gwamnonin jihohin Imo da Kogi tare da shugaban APC na ƙasa
- Shugaban ƙasan ya taya su murna, yana mai tuna musu cewa su zama bayi masu yi wa al'umma hidima da gyara jihohinsu
- Ya kuma bayyana zabukan da aka yi a jihohi uku a matsayin sahihai kuma waɗanda aka yi cikin kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci gwamnonin jam’iyyar APC da su rika sanya maslahar al’umma a gaba, su yi aiki tukuru domin inganta jihohinsu.
Shugaba Tinubu ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi bakuncin gwamnoni biyu da zababben gwamnan Kogi, Usman Ododo a fadarsa da ke Abuja, Channels tv ta ruwaito.
Gwamna Yahaya Bello na Kogi da takwaransa na jihar Imo, Hop Uzodinma, wanda ya lashe zabe a karo na biyu na cikin tawagar jiga-jigan APC da suka je wurin Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci zabbabun gwamnonin biyu, Ododo da Uzodinma, suka gana da Tinubu tare da wasu jiga-jigai.
Shugaba Tinubu ya yi musu nasiha
Da yake jawabi yayin ganawarsa da tawagar a Villa ranar Jumu'a, Shugaba Tinubu ya ce:
"Ku tabbata kun rungumi kowa kun tafi tare babu nuna wariya, yanzu kun zama bayi masu yi wa mutane hudima, kun yi aiki tuƙuru domin samun wannan nasara."
"Ku sani yanzu kun zama bayi masu yi wa jama'a hidima, godiya ta tabbata ga Allah bisa wannan nasara da kuka samu, ina rokon Allah ya dafa muku."
Tinubu ya ɗauki matsaya kan zabukan jihohi uku
Shugaban ƙasan ya bayyana jin dadinsa da sakamakon zaben jihohin Kogi, Imo da Bayelsa wanda ya ayyana a matsayin sahihi, na gaskiya da kwanciyar hankali.
Premium Times ta ce a sanarwan da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, Bola Tinubu ya ci gaba da cewa:
“Biyu daga cikin uku ba abu ne mara daɗi ba a karon farko, ba za mu mai da hankali kan cin zabe kadai ba, a’a, za mu mai da hankali ne ga al’umma domin kar mu ba su kunya."
APC ta yi nasara a shari'ar zaben gwamnan Kaduna
A wani rahoton kuma Kotun ɗaukaka kara ta kori karar PDP da Isah Ashiru, ta tabbatar da nasarar Malam Uba Sani a zaben gwamnan Kaduna.
Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, kotun mai zama a Abuja ta warware korafi biyar da masu karar suka gabatar.
Asali: Legit.ng