Gwamnonin PDP Sun Gana a Abuja, Sun Bayyana Matsayarsu Kan Hukuncin Tsige Gwamnoni 2

Gwamnonin PDP Sun Gana a Abuja, Sun Bayyana Matsayarsu Kan Hukuncin Tsige Gwamnoni 2

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bayyana kwarin guiwa cewa kotun koli zata yi adalci a hukuncin tsige gwamnonin Zamfara da Filato
  • Sun bayyana hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a matsayin wani koma baya na wucin gadi ga Dauda Lawal da Caleb Mutfwang
  • Kotun ɗaukaka dai ta bada umarci canza zabe a wasu yankunan Zamfara yayin da ta baiwa APC nasara a jihar Filato

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP ta yi imanin cewa kotun kolin Najeriya zata yi adalci a hukuncin tsige gwamnonin jihohin Zamfara da Filato.

Gwamnonin jam'iyyar PDP.
"Kotun koli zata yi wa Mutfwang da Lawal adalci" Gwamnonin PDP sun yi martani Hoto: @SenBalaMuhammed
Asali: Facebook

Idan baku manta ba kotun ɗaukaka ƙara ta Abuja ta rushe nasarar Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: An bankaɗo sabbon shirin NNPP kan wasu kusoshin APC a Kano bayan tsige Abba

Yayin da kotun ta umarci hukumar zaɓe INEC ta shirya sabon zaɓe a kananan hukumomi uku na Zamfara, ta ayyana ɗan takarar APC a matsayin gwamnan Filato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP sun cimma matsaya

Da suke martani kan wannan hukunci, gwamnonin jam'iyyar PDP sun ayyana tsige takwarorinsu a matsayin "wani tsaiko na kanƙanin lokaci."

Ƙungiyar gwamnonin PDP ta nuna yaƙinin cewa mambobinta guda biyun za su samu adalci a kotun koli, rahoton Daily Post.

Ta bayyana haka ne a wurin taron gwamnonin PDP wanda ya gudana a masaukin gwamnan jihar Bauchi da ke Abuja ranar Alhamis.

Taron ya samu halartar gwamnonin babbar jam'iyyar adawa guda shida yayin da wasu kuma suka turo mataimakansu a matsayin wakilai.

A sanarwan da suka fitar jim kaɗan bayan kammala tattaunawa, gwamnonin PDP suka ce:

"Taron ya yi nazari kan hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara ta yanke a baya-bayan nan game da gwamnonin Jihohi daban-daban da banbancin da aka samu."

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnoni 3, Kotun daukaka kara ta tsaida ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan APC

"A matsayin ƙungiya, mun jaddada kwarin gwiwarmu ga bangaren shari’a na yin adalci."
"Mun yi imanin cewa Kotun Koli za ta yi adalci a shari’o'in da muka samu koma baya na wucin gadi kamar jihohin Zamfara da Filato.”

Tinubu ya shiga tsakani a rikicin gwamna da mataimaki

A wani rahoton Bola Ahmed Tinubu ya shirya zama da mambobin majasar dokokin jihar Ondo ranar Jumu'a kan rikicin gwamna da mataimakinsa.

Wata majiya ta ce kafin wannan gayyata ta Tinubu, yan majalisun sun tsara zama da nufin sauke Gwamna Akeredolu su ɗora Aiyedatiwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262